Makarantar Ansarul Islamiyyat Da Ke Lokoja Ta Yaye Dalibai

Dalibai

Daga Ahmed Muhammed Danasabe,

A ranan Asabar data gabata ce, makarantar Madarasatul Ansarul Islamiyyat, bangaren haddar Alkur’ani dake Unguwar Kantimeti, a garin Lokoja, babban birnin Jihar Kogi, tayi bikin yaye dalibanta su shida.
Bikin dai ya samun halartan masu rawanin gargajiya da manyan malamai da kuma shehinan darikatul tijjaniyya sauran al’ummar musulmi dake garin na Lokoja.
Cikin wadanda suka halarci bikin sun hada da Wazirin Lokoja, Alhaji Abdulrahman Idris Babakurun da makaman Lokoja, Rear Admiral Ibrahim Dirisu da Shaban Budon, Injiniya Faruk Muhammed  da Wazirin Budon, Alhaji Ya Sumasu da kuma Sarkin malaman Lokoja Ustaz Abdullahi Mambo.
Sauran sune babban limamin garin Lokoja, Sheikh Muhammadu Aminu Sha’aban da Sheikh Yusuf Abdulkadir Zariya da Sheikh Yahaya Abdullahi Soje da  malam Mahmuda Sardaunan Faila  da  Alaramma Abdulrahman Danladi Kabawa da kuma sauran al’ummar musulmi.

Da yake jawabi a wajen bikin, Sheikh Kalifa Shaibu Ibrahim Kenchi wanda har ila yau shine Magajin Garin Lokoja, kira yayi ga iyaye dasu tashi haikan wajen ganin sun baiwa ya’yansu ilimin addinin musulunci, musamman ilimin Alkur’ani mai tsarki domin ganin sun samu rabo a nan duniya da kuma can lahira, yana mai cewa idan an rasa Alkur’ani mai girma, tamkar an rasa duniya da lahira ne.
Yace Alkur’ani mai tsarki na wanke kwakwalwar yara kuma shine tsani na samun ilimin boko, inda ya kara da cewa samun ilimin Alkur’ani ga yara yana kare su daga zama kangararru a cikin al’umma.
Magajin Garin na Lokoja ya kuma kara da cewa akwai dimbin lada ga mai karanta Alkur’ani da kuma mai sauraron karanta shi, sannan ya nanata da cewa Alkur’ani  waraka ne ga kowace matsala a rayuwa.
A saboda haka ya shawarci musulmi dasu rungumi Alkur’ani mai tsarki tare da kuma yin kira ga masu hannu da shuni dasu rika tallafawa makarantun addinin musulunci da malamansu.
A karshe Sheikh Shaibu Ibrahim Kenchi, ya taya daliban da aka yaye sannan ya bukace su da ci gaba da rungumar Alkur’ani mai tsarki.
A nasa takaitaccen jawabin, shugaban bikin, Shaban Budon, Injiniya Umar Faruk Abubakar, wanda Alhaji Ya Sumasu ya wakilta tunda farko, sai da ya taya dalibai da iyaye da kuma mahukuntar makarantar murna, sannan yayi alkawarin tallafawa makarantar.

Shugaban makarantar ( Principal), Malam Musa Lukman Yabagi yace makarantar ta fara ne da dalibai 47 shekaru uku da suka shude,amma a yanzu dalibai goma sha daya ne kacal ke karatu a makarantar.
Malam Lukman Yabagi wanda ya koka matuka da yadda wasu iyaye ke yiwa karatun ya’yansu rikon sakainar kashi saboda gaza biyan kudin makarantar yaran wanda bai taka kara ya karya ba, ya kuma yi kira ga iyayen dasu kara kokari da sa himma wajen kula da karantun ya’ yan nasu, musamman ma ilimin Alkur’ani mai tsarki.
Daga nan yayi kira ga masu hali da kuma sauran al’ummar musulmi dasu tallafawa makarantar ta Madarasatul Ansarul Islamiyyat , inda kuma a karshe ya godewa dukkan al’ummar musulmi da Allah ya basu damar halartan bikin.
Daliban da suka yi haddar Alkur’anin kuma aka yaye a bikin, sun hada da Ibrahim Isah da Isah Bashir Yabagi da Yahaya Abubakar da Alkali Isah Yabagi da  Ummu Hani Bashir Yabagi da kuma Hajara Abubakar.

Exit mobile version