Daga Alhussain Suleiman
Yanzu za a iya cewa makarantar kimiyar lafiya ta jihar Kano, ‘School of Health Technology’ ta shiga sahun makarantun kimiyar lafiya da suke tafiya dai dai da zamani a kasar nan idan ka kwatanta da shekarun baya.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin shugaban makarantar Alhaji Bello Danhatu, a lokacin da yake zanatawa da manema labarai a ofishin shi da ke makarantar kwanakin baya. Alhaji Bello danhatu, ya ce shigowar shi makarantar ya ga ana tafiyar ba dai dai da zamani ba, ya ce ida kana son ka yi adalci tsakanin daliban makaranta sai ka koma tsari irin wanda zamani ya zo da shi musamman tsari na yanan Gizo.
Kan haka sai ya yi magana da ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, inda ta aminci aka sanya makarantar akan yanar Gizo, tanan daliban suka sayi fom suka cike ta wannan tsarin ne aka tantance su sannnan kuma suka yi jarabawa akan kwamfutar mai makon tsarin da ake yi shekara da shekaru ba tare da kwamfuta ba.
Har ila yau da zuwan shi ya samar da karin kwasa kwasai har guda takwas wanda ba’a yin su amakarantar sannan kuma an kara yawan daukar dalibai , wanda matukar kana son ka taimaka ta hanyar ilimi ne za ka taimaka domin tanan ne za’a iya gane mai ilimi da wanda ba shi das hi.
Malam Bello Danhatu, ya tabbatarwa da nmanema labaran cewa makarantar yanzu haka tana da kwararrun malamai wanda kowa ya kware akan fannin day a karanta , wannan ya sa makarantar take alfahari da su sabodahaka ya jinjinawa malaman akan yadda suke ba shi hadin kai da goyon baya domin makarantar ta ci gaba .
Sannan kuma daliban makarantar maza da mata suna da tarbiya tare da mayar da hankulan su akan karatu da fatan hakan zai dore