Makarantar Koyon Sana’ar Hannu Dake ‘Yankara Ta Yaye Dalibai Karo Na 11

Sana'ar

Daga Abdullahi Sheme,

A makon da ya gaba tane makarantar koyar da sana”oin hannu ta garin ‘Yankara dake karamar hukumar Faskari a jihar Katsina ta kara yaye dalibanta karo na 11 a harabar makarantar a garin na ‘Yankara.  Tun da farko a nasa jawabin, shugaban makarantar Malam Galadima Dantsafe shi ne kuma Farin Ganin Sarkin Yamman Faskari ya yi dogon jawabi na tarihin kafa makarantar inda ya ce, yanzu sun yaye dalibai sama 120 tun kafuwar makarantar wani bawan Allah mai kishin mahaifarsa da al”ummar yanki ne ya kafa makarantar, mai suna njiniya Alhaji Shehu Sallau Yankara Wakilin Wajen Katsina, ya ci gaba da cewar yau  kimanin shekaru 11 kenan da fara koyawa mata sana”oin hannu sana”oin sun kunshi koyar da dinkin keke da koyar da sakar hannu da yin manshafawa da turaren kamshi na fesawa a dakuna da ruwan omon wanke wanke da koyar da gyaran gashi na mata da dai sauran sana’oi shugaban makarantar ya ci gaba da cewar wannan makarantar tana koyawa matan aure da ‘yammata da zawarawa musamman wadanda a ka kashe masu mazaje da ‘yan ta”adda suke yi a wannan yanki namu mai albarka duk abinda wannan makaranta take da shi na koyarwa kamar irinsu sinadiran da a ke hada sabulan wanka da wanki da na turaren kamshi da atamfofin da a ke yankawa don koyawa matan dinki da zaren dinki da duk abinda za a nema don yin aikin wanda ya kafa makarantar ya samar da su kyauta ya ce tuni ya sanya manyan kekunan dinki a wannan wurin koyar da sana”oin hannun Dantsafe ya ce, babu abinda za su cema wanda ya kafa wannan makarantar watau, Alhaji Shehu Sallau ‘Yankara Sarkin fadar ‘Yankara

Barayan Faskari kuma shi ne Wakilin wajen Katsina sai godiya da fatan alkhairi kuma Allah ya biyashi da mafificin lada irin wadannan bayin Allah a keso a cikin al”umma saboda taimakonsu daga nan ya mika godiyarshi ga wani bawan Allah Alhaji Abdulkadir Aliyu Faskari AK wanda ya taba  ba makarantar gudunmawar kekunan dinki guda 10 don a cigaba da koyama matan sana”oin ya ce wannan ba karamin abin a yabo bane daga nan ya yi kira da babbar murya ga masu hannu da shuni da manyan ‘yan boko da manyan manoman yankin su kawo gudunmawarsu don matan yankin su dogara da kansu a nashi jawabin wanda ya kafa makarantar Injiniya Alhaji Shehu Sallau ya ce kishin gida  da son ganin kowa ya tashi ya dogara da kanshi yasa ya kafa wannan makarantar don koyawa iyayenmu sana”a musamman mata domin sune suke dawainiya da gidajenmu da tarbiyar da yaranmu kuma ta haka ne za a magance tallar da kananan yara ‘yam mata ke yi wasu ta hanyar talla ne a ke yi masu fyade.

Wakilin Wajen Katsina ya cigaba da cewar yana kishin mahaifarshi da jama”ar yankinsu kuma jama”a su tashi tsaye su dogara da kawunansu sannan ya yi kira ga yan boko da masu hannu da shuni su dawo gida su taimaki jama”a su yi koyi da mutane masu kishi ba a koma gefe guda a na surutai ba ya kara da cewar mu fito mu hada karfi da karfe don mu ciyar da al”ummar gaba daga karshe an raba kyaututtuka ga matan da suka yi kwazo wajen koyon sana”oin mutane da yawa suka yi jawabai a wurin yaye daliban kamar irinsu Alhaji Ali Musa ‘Yankara Danmasanin ‘Yankara da Malam Aminu. Mairuwa sannan a ka kaddamar da saida takardun cikewa na shiga makarantar karo na 12 an yi addi”oi na samun zaman lafiya a yanki da halartar manyan baki da yawa da suka zo daga wurare daban daban.

 

Exit mobile version