Ibrahim Muhammad" />

Makarantar Sheik dahiru Bauchi A Kano Ta Yaye Yara Mahaddata 159

Makarantar Sheik dahiru Bauchi dake Kano ta yi saukar haddar kur’ani na yara 159 a sabon harabar makarantar na dindindin dake unguwar Tudun Yola.
Da yake jayawabi a wajen taron wanda ya wakilci Gwamnan Kano tsohon mai bai wa Gwamna Ganduje shawara a kan cigaba daga al’umma, Alhaji Yusuf Tunfafi ya bayyana fatan alherin Gwamnan Kano ga masu saukar da makarantar.
Ya ce, Gwamnatin Kano tana da kuduri na ba irin wannan makarantu kulawa don daukewa dalibai da malamai nauyi.
Akwai hukuma dake kulawa da irin wadannan makarantu na addini anyi rijistar makarantun Islamiyya guda 130,000 da za’a ba su kulawa ta tsarin.
Shima a nasa jawabin malami da ya yi darasu ga wadanda suka yi haddar kuma shugaban makarantun na sheik dahiru Bauchi Sheik Ibrahim Sheik dahiru ya bayyana muhimmancin karatun kur’ani.
Ya ce, makarantun a karkashinsu sun kai 200 a ciki da wajen kasarnan da take bada ilimin haddar cikin shekaru hudu.
Sheik Ibrahim ya ce, a kasar Ghana da ya je saukar kur’ani na wannan makarantar reshen kasar na mahaddata uku saida mataimakin shugaban kasar ya halarta.
Tunda farko a jawabinsa na maraba shugaban makarantar na Kano Sheik Dokta Abubakar (Srimbai) Sheik dahiru Bauchi ya yaba wa masu bada gudummuwa ga cigaban makarantar da iyaye da malamai.
Ya ce, makarantar tana daga makarantu na Sheik dahiru Bauchi dake ciki da wajen kasar nan kuma anan kano tana da rassa da yawa Sheik Abubakar ya ce, yara da ake kawowa a shekaru hudu suke haddar kur’ani kuma saukar shi ne karo na 12 tun daga kafa makarantar a 1999.
A wannan saukar na 12 shi ne mafi yawan dalibai. Yaja hankalin iyaye su cigaba da taimakawa da kawo bulo don gina sabon matsugunin makarantar da aka kewaye aka soma ginata da irin tallafin kawo bulo da ake.
Da yake zantawa manema labarai daya daga iyaye da suka halarci saukar daliban na makarantar.
Alhaji Abdulkadir Aminu ya yi godiya ga Allah sauka da makarantar Sheik dahiru Bauchi karo na 12 suna farin ciki da wannan abu. Ya ce, wannan abu da Allah ya nuna musu abin farin ciki ne saboda Shehi dahiri Bauchi yana bada gudummuwa ga cigaban addini daba abinda za’a ce sai Allah ya saka masa da alkhairi.
Alhaji Abdulkadir Amin wanda akafi sani da Umar Ladiyo ya gode wa malamai da suke taimakawa, da fatan Allah ya cigaba da basu kwarin gwiwa su kuma iyaye Allah ya kara musu himmar sa yara kan tafarkin kur’ani.
Alhaji Abdulkadir Amin ya ce, abin farin cikine da ba za su manta da shi ba domin duk mutuminda ya riki Alkur’ani Allah ya gama yi ma sa komai.
Shima a nasa bangaren Alhaji Bashir Bello yaja hankalin al’umma su rika taimakawa irin wadannan makarantu ta duk wani mataki da ya kamata ayi.
Ya ce, mutane dake haddasa irin wadannan makarantu ba karamin aikin alkhairi ba ne domin domin dinbin yara da ake tarbiyantar dasu.
Da masu hali da iko za su dukufa wajen tallafawa ilimi da ta’addanci da ake fama dashi zai zama babushi a kasar nan.
Alhaji Bashir ya taya iyayen yara murna da Allah ya basu ikon sauke nauyin da Allah ya dora musu kan yaransu duk wanda yake da yaro ya kawoshi irin wannan makaranta domin samun tarbiyya

Exit mobile version