Sagir Abubakar" />

Makarantun Islamiyya Sun Samu Tallafi A Katsina

Dan majalissa mai wakiltar karamar hukumar Katsina a majalissar dokokin jaha ta yi alkawarin tallafama makarantar Islamiyya ta Darussahaba dan magance wasu matsaloli da makarantar ke fuskanta.
Alhaji Aliyu Abubakar Albaba ya bayyana hakan ne a lokacin bikin yaye daliban makarantar karo na (6) wadanda suka hardace Al-kur’ani mai tsarki wanda ya gudana a harabar makarantar.
dan majalissar ya shawarci iyaye akan su dunga biyan kudin makaranatr ya’yansu a koda yaushe don bama hukumar makaranta damar tafiyar da lamurran ta yanda ya dace. Ya bayyana Islamiyyar a matsayin mai taka muhimmiyar rawa wajen tarbiyyar yara da matasa a cikin al’umma.
Tun farko a jawabin maraba mataimakin shugaban kwamitin gudanarwar makarantar Malam Naziru Sani ya ce makarantar na da dalibai yara kanana sama da (420) da suka kunshi maza da mata da kuma matan aure.
Ya bayyana wasu daga cikin matsalolin da suke damun makarantar da suka hada da karancin azuzuwan karatu. Ya kuma nuna godiyarshi ga goyon bayan da wasu daidaikun mutane ke ba makarantar da yake taimakawa wajen tafiyar da ita yadda ya dace.
Da yake gabatar da kasida babban limamin masallacin juma’a na rukunin gidajen Goruba dake nan Katsina Dr. Abba Bala Gambarawa ya bayyana cewa wadanda suke rike da madafun iko da kuma iyaye suna da muhimmiyar rawar da zasu taka wajen samar da ingantaccen ilimin addini ga yara kanana.
Sai ya bukaci iyaye akan sanya ‘ya’yansu Islamiyya domin samun ilimin addini. A wajen bikin an gudanar da karatun kur’ani mai tsarki, an kuma bada shaidar yabo da kyaututtuka ga dalibai da malamai dama wasu daidaikun jama’a.

Exit mobile version