Haruna Akarada" />

Makarantunmu Na Bukatar Tallafin Gwamnati – Jammaje

A ranar Litinin ta makon jiya marubucin littafin nan, MALAM KABIRU MUSA JAMMAJE, ya kaddamar da wani littafi mai dauke da kalmomin Turanci 1,000 da ma’anarsu. Dalilin samar da wannan littafi dai akwai wani shiri da ya ke gabatarwa a gidan rediyo Freedom. Wannan ne ya sa mutane su ka yi ta kiraye-kiraye da a maida shi littafi. A karshe dai Malam Kabiru Jammaje ya amince da bukatar jama’a ta wallafa littafin, domin mutane su ilimita.

Wakilin LEADERSHIP A YAU, HARUNA AKARADA, ya samu ganawa da Jammaje bayan kammala taron kaddamar da littafin a birnin Kano. Ga dai yadda hirar ta kasance:

Meye makasudin wannan taro?

Dalilin wannan taro shi ne na fito da wani littafi mai kalmomi 1,000, wanda na ke gabatarwa a Freedom Radio da ke Kano. Sunan littafin The 1000 Words.

Dalibai za su yi amfani da shi ne ko kuwa iya makarantarka kadai?

Ba iya makarantata ba ne; duk mai shaawa ko a wacce makaranta ya ke, zai iya dauka ya karanta.

Wane kira ka ke da shi wajen zaburar da iyaye, domin su cigaba da tura yaransu zuwa makaranta?

Mun dade mu na kira ga iyaye, domin Arewa an bar mu a baya. Gaskiya sai mun tashi tsaye wajen ganin iyaye sun cigaba da tura yara zuwa makaranta. Lallai ya na da kyau mu kara dagewa, mu kara zage damtse sosai da sosai. Kusan rayuwuta gabadaya na tashi ne wajen yi wa mutane hidima a kan su tashi su yi ilimi, domin shi ilimi abu ne da ya kamata kowa ya yi shi. Da wannan ne mu ke samun cigaba a duk al’amura. Idan yanzu ba mu yi ba, to nan gaba sai an yi ma na dariya. Ka ga wannan ai matsala ne. Ni kaina yanzu ban san iya yawan dalibaina ba. Shi ya sa rayuwata ta tafi a karance-karance. Idan ba ka yin karance-karance, ba za ka san komai ba. Dole mutum ya zama mai karance-karance. Abinda b aka sani ba, sai ka sani.

Ka dade kana koyar da dalibai. Shin akwai wani shiri na gina wata katafariyar makaranta, domin ganin yadda ka yi suna a harkar bada karatu a nan jihar Kano da ma wasu gurare?

In sha Allah, duk da abu ne mai tsada, zan amfani da wannan damar ma; mu na kira ga gwamnati ta shigo, domin ta tallafa ma na. Dalili shi ne, abinda mu ke karba a wajen dalibai bai taka kara ya karya ba. Wannan kudi da shi mu ke biyan kudin haya, da shi mu ke biyan malamai da sauransu. Idan gwmnati ta kalli wannan, ta na iya taimakawa da wani abu, domin mu kuma mu cigaba da tallafa wa al’umma.

Sau da yawa za a yi ta kira, domin irinku masu kokarin taimaka wa al’umma, amma sai a yi ta kira, amma ka ji shiru. Me za ka ce a kan wannan?

Gaskiya haka ne; irin wannan sai ka yi ta fada, ka yi ta fada, amma sai ka ji shiru, amma ba za mu gajiya ba; za mu yi ta fada har maganar ta kai kunnen ita gwamnati. Kuma ba ita kadai ba, duk wanda ya ga ya na da gudunmawar da zai bada, shi ma ya bayar.

Ka na daya daga cikin masu shirya fim din Turanci. Mene ne dalilin shirya fim, duk da ga shi kai malamin makaranta ne?

Gaskiya ne na shirya fim da dama. Gaskiya yawanci finafinaina a kan ilimi ne, kuma da fara yi na sanya tunanin mutane da dama a kan wannan harka ta fim da na shiga. Za ka ga na nuna a kyale mata su je su yi karatu. Kuma abin ya yi tasiri kuma mun yi amfani da wannan finafinai wajen koyan Turanci ma. Da ma fim dina da Turanci na ke yi, domin karuwarmu. Kuma ’yan Kudu, sako ya fara isar mu su cewa ’yan Arewa ma su na yin fim da Turanci. Daga wannan finafanai su ka san cewa, Arewa ma akwai gwanayen iya Turanci.

Wane kira ka ke da shi na karshe?

Kirana shi ne wannan littafi da ya fito kowa ya mallaka, domin maganar da na yi cewa a mallaki wannna littafi, zai taimaka wa karatu a koda yaushe. Wannan ne ya sa mu ka dage, domin ganin wannan al’ummar ta yi karatu; mazansu da matansu. Shi ya sa mu ke kara kira ga gwamati da ta taimaka wajen dauke ma na wasu abubuwan, domin cigaban ilimi da kuma samar da zaman lafiya, saboda idan a ka samar da ilmi, mutane su ka samu tarbiyya, ba za a dinga matsaloli a cikin a’lummar nan ba.

Exit mobile version