CRI Hausa">

Makiyaya A Jihar Mongoliya Ta Gida Ta Kasar Sin Sun Samo Sabuwar Hanyar Samun Wadata

Naran-Mandakh, wani makiyayi a gundumar Huhemudu dake birnin Ordos na jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kai ta kasar Sin, kwararre ne wajen kiwon shanu da kaguwa. A shekarar da ta wuce, yawan kudin shigar da ya samu ya zarce kudin Sin Yuan miliyan 3.

A baya, shanu da ragunan da ya kiwata ba su da isassun ciyayin da za su ci, amma ana samun sauye-sauye a shekarun nan.
A shekara ta 2014, an janyo ruwa daga rawayen kogi wato Yellow River don ya malala cikin hamadar Kubuqi, abun da ya sa muhallin halittun dake hamadar ya kyautata kwarai da gaske. Ruwan da ya shiga yankin ya sa ciyayi suka rika fitowa, har dabbobi suka samu isasshen abinci, shi kuma Naran-Mandakh ya fara sana’ar kiwon kaguwa.
Shugaban hukumar kula da harkokin ruwa dake wurin, Liu Haiquan ya bayyana cewa, a baya, ana fama da matsalar kwararar hamada, gami da ambaliyar ruwa. Yanzu ruwan da aka shigar hamadar ya kyautata muhallin halittu, har yankin hamada ya zama wuri mai ni’ima. Mista Liu Haiquan ya kara da cewa, muhallin hamadar Kubuqi ya samu ingantuwa kwarai da gaske, har ma ana kara samun halittun dake rayuwa a wannan wuri, kuma sana’ar kiwon dabbobi da Naran-Mandakh yake gudanarwa tana ci gaba da habaka. A shekara ta 2006, shanu 20 kadai ya kiwata, amma yanzu adadin ya zarce 700. (Mai Fassara: Murtala Zhang)

Exit mobile version