Makiyaya Sun Kashe Tare Da Bizne Abokinsu A Ogun

Daga Khalid Idris Doya

Wasu ‘yan bindiga sun shiga hannun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun a bisa zargin laifin yin garkuwa gami da hallaka wani ɗan bindigan mai suna Taye Amodu.

Ta ɓangaren ‘yan sandan, waɗanda ake zargin dai sune Hassan Amodu da Abubakar Abdullah waɗand ake zarginsu da haɗa baki wajen yin garkuwa da Amodu a ranar 23 ga watan October, 2017 a yankin Obada Oko da ke Abeokuta gami da yin awun gaba da shanu guda takwas.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun Abimbola Oyeyemi, ya ce iskowar labarin garesu ke da wuya ne kuma nan take kwamishinan ‘yan sandan jihar CPAhmed Iliyasu ya umurci shugaban sashin daƙile aikace-aikacen ‘yan fashi da makami, DSP Uba Adam domin su taso ƙeyar waɗanda ake zargin.

Ya ce: “wajajen ƙarfe 5:30 na yamma a wannan ranar ne ‘yan SARS suka yi ram da su a wani waje a yankin Imeko. Inda aka samu yin ram da su a wani daji da suke buya. Dukkanin waɗanda ake zargin su biyu dukkaninsu an kamo su. Ababen da aka kamusu da su sun haɗa da bindiga da alburusai, da kuma adduna”.

Ya ce: “a yayin da muke tsaka da gudanar da bincike a kansu gami da yi musu tambayoyi sun amsa da kansu cewar sune suka kashe wanda suka kashen sakamakon ya basu wahala a lokacin da suke ɗauke da shi hakan ne kawai ya sa suka hallakasa, gami da bisne gawarsa a cikin wani rami mai zurfi a wani daji. Haka kuma sun bayyana da bakinsu sun yi awun gaba da shanunsa guda takwas”. In ji PPRO

Mai magana da yawun ‘yan sandan Ogun wato Oyeyemi ya shaida cewar suna nan suna ci gaba da shirye-shiryen gurfanan da waɗanda ake zargin a gaban kuliya domin fuskantar shari’a daidai da laifukansu bayan ‘yan sandan sun kai ga kammala bincikensu kan lamarin.

 

 

Exit mobile version