Connect with us

MANYAN LABARAI

Mako Mai Zuwa Za A Sassauta Dokar Zirga-zirga A Abuja –Buhari

Published

on

A Jawabin da shugaban kasa Buhari ya gudanar sa daren nan, Shugaban ya ce za sassauta dokar hana zirga-zirga a jihohin Legas, Abuja da Ogun wanda suka shafe makonni hudu suna cikin dokar hana zirga-zirgar.

Sannan Shugaban ya bayyana cewa an sanya dokar hana Zirga-zirga ta tsawon makonni biyu, sai kuma dokar takaita zirga-zirga a fadin Nijeriya wanda dokar za ta fara daga karfe 9 na safe zuwa 6 na yamma a fadin Nijeriya.

Sai kuma dokar hana balaguro a tsakanin jihohin Nijeriya gaba dayansu, sai kuma kokarin gwamnatin na tilasta sanya takunkumin fuska wato “Face Masks. A duk fadin Nijeriya. A karshe kuma an sanya dokar hana zirga-zirga daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: