Makomar Tsaro A Arewa

Jami'an Tsaro

Kwamared Sunusi Mailafiya,

Al’umma har sun fara gajiyawa da karanta duk wani sharhi da ya danganci tsaron Kasar nan, musamman bangaren Arewa. Domin abune da har yanzu an kasa shawo kansa duk da makudan kudaden da ake futarwa da sunan dawo da tsaro a wannan kasa tamu. Tun lokacin da aka sace yaran Makarantar GSS Kankara, zuciyata ta yi laushi, jikina ya mutu, sannan kuma na gaza gano dalilai da suka sanya har kawo yanzu tsahon shekaru 11 an gaza gano ta ina za a shawo kan abun. Hakan ya kuma tuna mana da irin salon da aka yi aka sace ‘yan Makarantar Chibok da Dapchi. Wannan tamkar wata yar manuniya ce cewar har kawo yanzu yan ta’addan kasar nan sun gagari Gwamnati. Wannan kenan.

Rashin tsaron yanzu haka ya sanya al’umma dakatar da duk wata zirga-zirga walau ta kasuwanci ko ta zumunci, kawai don tsira da rayukan su. Yau ta kai ta kawo manyan titunan kasar nan sun zama tamkar kufe saboda yadda al’umma suka kaurace musu, titunan Kaduna, Abuja, Katsina, Zamfara da Sokoto sun gagari jami’an tsaro wajen damke masu garkuwa da mutane, haka suma al’umma sun kaurace musu saboda tunanin me zai iya faruwa. Wani abun tashin hankali ma shine yadda da yawan lokuta duk wanda aka dauke musu ahali, babu abinda ya rage musu illa kokarin tattara kudaden da yan garkuwar suka nema, saboda kawai su fanshi ahalin nasu, domin kuwa duk wani kokari na jami’an tsaro sam baya amfani, ballantana su ji cewar za’a kubuto musu da wanda aka kama, idan kuwa wani sa’in yazo da rashin sa’a, ko kun biya diyyar da aka nema, sai su hallaka ahalin naku.

Idan muka dubi adadin daliban Chibok da na Dapchi yadda aka tattara su tamkar wasu awaki, wani zaiyi uzurin cewar lokacin Boko haram na da karfi ne, to amma a yanzu da kusan Gwamnati take ayyana cewar ta ga karshen su, shin ta yaya hankali zai dauka cewar an tattara daliban da suka haura dari biyar, har kuma yan ta’addar su kaisu sansanin su batare da jami’an tsaro sun dakatar dasu ba. Dole mai hankali ya tambaya shin har sakacin jami’an tsaron Kasar nan ya kai haka?.

Kamar ko yaushe Gwamnati itace wacce al’umma suka dora duk wata yardar su da amincewa cewar sune zasu samar musu da tsoro, domin itace take da jami’an tsaro. Sannan kusan kowane lokaci muna karanta yadda ake kashe makudan kudade da sunan warewa bangaren tsaro, tun daga kan kudaden siyo makaman da zasuyi amfani dasu, amma ace har kawo yanzu ana sace al’umma, ana bude musu wuta kan me uwa-da-wabi, tare kuma da awon gaba da daliban makaranta masu dinbin yawa, tabbas wannan abin tashin hankali ne.

Gwamnatin APC tayi yakin neman zabe da samar da tsaro, tare da alkawarin kawo karshen Boko haram da ta gada daga Gwamnatin Mai Malafa (GEJ), to amma fa al’umma yanzu sun fara gane cewar ba lalle hakan ya tabbata ba, musamman ganin kusan shekaru har 6 akan mulkin, kusan babu wani abu daya canza, abu mafi muni shine yadda Talakawa ne suke dandana kudarsu daga azzaluman yan ta’adda, wannan take nuna tamkar sunfi karfin Gwamnati. Talakawa da dama sun ajje duk wata soyayyar su ga Gwamnatin PDP, duk da irin kyautayi da suke ganin tayi musu, amma suka tsaya kai da fata cewar sai sun canza, sun kawo wanda zaiji kansu, sai gashi wankin hula yana neman kai su dare.

Al’umma da dama sunyi kira da Gwamnatin Tarayya da ta sallami Shugabannin Rundononin tsaron Kasar nan, tun daga yan jam’iyyar adawa har zuwa cikin jam’iyya me mulki, Dattawa da sauran masu sharhi suna ganin canza Serbice Chiefs zai bada dama wajen amfani da wasu hanyoyin don kawar da yan ta’adda, domin kusan wanda suke kai zahiri sun gaza wajen kokarin su. To amma har yanzu na rasa dalilan da suka sanya fadar Shugaban Kasa tayi kemadagas wajen karbar koken al’umma, sunyi biris tare da ganin har yanzu tamkar za su iya yin wani abin kirki, duk fa da cewa kusan kullum sai munji mummunan labari akan sace wasu, ko kuma kashe wasu babu gaira ba dalili. Kai ko iya kisan gillar da aka yiwa yan’uwanmu a Zabarmawi, ya isa Gwamnati tagane cewar manyan jami’an tsaron data amince dasu, tabbas abin yafi karfin tunanin su, to bamu fa gama wannan jimamin bane, kawai sai ga satar yaran GSS Kankara, suna dawowa kuma, sai ga satar wani Attajiri da wasu ahalinsa a garin Falgore, sai ga Minjibir kuma, duka wadannan munanan labaran sun faru ne cikin kasa da kwana ashirin, amma duk da haka wadannan Dattijan da suke jagorantar rundunonin tsaron kasar nan suna ganin babu wanda yafi su kokari, kuma idan har babu su, suna ganin tashin hankalin sai yafi haka.

Ya kamata a iya shekarun da suka ragewa Baba Buhari ya canza salon yadda yake son dakile ta’addanci da kashe-kashen al’umma a kasar nan. Idan har za’a iya rushe rundunar SARS ta yan sadda saboda ana tunanin suna wuce gona da iri, to tabbas ya kamata sauran jami’an tsaron Kasar nan da kawar da yan ta’adda yake nauyin su, suma ayi musu garambawul. Inaga wannan itace hanya kadai da zata nuna cewar wannan Gwamnatin da gaske take wajen kawo karshen ta’addanci da kashe-kashen al’umma a kasar nan.

alimailafiyasunusi@gmail.com – 08036064695

Exit mobile version