Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Uwar Gidan Gwamnan Jihar Kano, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje, ta kara tunatar da mata muhimmancin zuwa awon ciki da kuma kula da alluran riga-kafin da ake yi wa kananan yara.
Farfesa Hafsat Ganduje ta yi wannan tunatarwa ne a lokacin da ta ke kaddamar da makon duba lafiyar mata masu dauke da juna biyu da kananan yara wanda Gwamnatin Jihar Kano ta shirya karkashen Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano.
Ta kuma kara da kiran maza da su rika tausayawa matansu masu Juna biyu ta hanyar kulawa da ba su abinci mai gina jiki da kara lafiya.
Bayan nan ta raba kyaututtuka da kayan abinci masu gina jiki ga matan da suka zo asibitin, domin yin awo da kawo yara rigakafi.
A nasa jawabin, Kwamishinan Lafiya, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya ce kasancewar cutar kyanda na saurin hallaka kananan yara ya sa Ma aikatar Lafiya ta Kasa ta mayar da yin rigakafi sau biyu ga kowane yaro a wata.
Dakta Tsanyawa ya kuma ce Ma’aikatar Lafiya za ta ci gaba da yaki da cutar tarin fuka da cutar yunwa da kuma cutar corona da dukkan cutar da ke saurin yaduwa a tsakanin al’ummah.
A nasa bangaren, mai Martaba Sarkin Rano, Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa, ya yi karin haske ne bisa yadda ake karbar alluran a garin Rano tare da yin kira ga mata masu juna biyu da su mayar da hankali wajen cin abinci da zai kara lafiyar su da abinda su ke dauke da shi acikinsu su kuma rika zuwa awon ciki. Kamar yadda Jami’ar yada labaran Ma’aikatar lafiya Hadiza Mustapha Namadi ta shaida wa LEADERSHIP A Yau.