Makon Yaki Da Shan Miyagun Kwayoyi: Matsalar Shaye-Shaye Na Da Tasiri Wajen Lalata Tarbiyar Al’ummarmu – Sarkin Arewa

Wannan tattaunawa ce da LEADERSHIP A YAU ta yi da daya daga cikin shugabannin al’umma a bisa munasaba da wannan mako da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe musamman domin yaki da tu’ammuli da miyagun kwayoyi a duniyar nan. ALHAJI ABDUL’AZIZ SALISU MAI MAGGI, wanda shi ne Sarkin Arewan Anguwar Mu’azu a Kaduna, basarake ne kuma dan kasuwa. Ya zanta da wakilinmu, UMAR A HUNKUYI, a kan mahimmancin wannan makon, inda Hunkuyi ya jefa wa Mai Maggi tambaya guda, wacce ya bada doguwar amsa a kanta. Ga dai yadda Uban Kasar ya bayyana yadda tarbiyya a kullum sai kara lalacewa ta ke yi sanadiyyar shaye-shayen. A sha karatu Lafiya:

Me za ka ce game da dalilin lalacewar tarbiyya a cikin al’umma?

Dalilin lalacewar tarbiya a tsakankanin mu, wannan ya faru ne sakamakon nuna halin ko-in-kula da manya da kuma matasa gabaki-daya suka nuna a kan tarbiyan da muka samu tun daga iyaye da Kakakanni. Akwai Hadisin Ma’aikin Allah (S) da yake cewa; Duk wanda bai girmama na gaba da shi, bai kuma tausaya wa na kasa da shi, Annabi ya ce ba shi tare da shi. Da yawa mutane mun bar wannan turban an koma ana rayuwa kamar ta dabbobi.

To zuwan Bature, duk da ya zo ya yi shekarun da ya yi, ya wuce, sai ya zama al’ummar Musulmi sun kasu kashi-kashi, da yawa sakamakon danniya da aka samu na Sarakuna wanda ya kara gurbata al’umma suke ganin a maimakon a ce Sarakunan sun zama iyayen su sai suke ganin sun zama tamkar abokanan gabansu.

Daga baya kuma sai ya zama ‘yan siyasa suka salladu a kan kowa, sai kuma abin ya kara gurbacewa, domin dan siyasa yana neman jama’a ne wadanda za su biya ma shi muradunsa kadai, walau muradun nan na shi su kasance masu kyau ko marasa kyau ne. ‘Yan siyasa sun fito da kudade sun baiwa yara kanana, da haka suka sanya su a cikin bangar siyasa, suka ba su kwayoyi da sauran kayayyakin da ke haddasa maye suna gusar masu da hankula, ya zamana dan siyasa ne kawai ake gani mutumin kirki, shi ma saboda zai dauko ya bayar, attajiran da suke zaune a gari ko a Anguwa duk aka dauke su mutanan banza, domin abin da dan siyasa zai iya daukowa ya bayar babu wani dan kasuwa ko attajiri da zai iya ba ka kamarsa. Saboda shi duk abin da zai ba ka ya san nawa ne ya samu, nawa ne kuma yake kashewa. Shi kuma wancan ya samu ne daga cikin gumin al’umma, don haka ma bai damu da makomar al’ummar ba matukar dai zai biya wa kansa bukatarsa, to ko ma mai zai faru ya faru, wannan yana daga cikin abin da ya kara rusa mana tarbiya.

Dan siyasa ya baiwa mutane kudi sun kuma bayar da dama an shigo da kwayoyi, da kayayyakin da ke sa maye, su ke bayar da izini a yi doka, su ne kuma farkon wanda ke karya ta. Wannan sai ya sanya tun daga shigowar siyasa zuwa yanzun, kullum tarbiyar sai kara tabarbarewa take yi. Don in ka kama mutum ka kai shi wajen jami’an tsaro, to su dai wadannan ‘yan siyasan da yawansu ba mu ce duka ba, su ne dai wadanda za su je su yiwo belinsa, ya dawo cikin al’umma yana tinkahon cewa duk mutumin ma da ya sake sanya ma shi ido zai dauki mataki a kansa. Cikin al’umma da yawa an san wanda ya yi kisan kai an kama shi an tabbatar shi ma ya yi ikirari da bakinsa an tafi da shi, amma bayan kwana biyu sai ka ganshi ya dawo yana yawo a cikin al’umma. Yanzun da shike abin ya yi yawa ma sosai, kusan kowace Anguwa a sarari yake an san wuraren da ake tu’ammuli da mugayen kwayoyi.

Wannan akwai bambanci da tsari na Sarakuna, domin mutum ko da za ka samu yana yin abin da ba daidai ba, amma za ka samu yana kokarin kiyaye wannan alfarmar da aka ba shi, domin shi ya san uba ne na kiyaye Addini da al’adar da aka dora shi a kai, sabanin dan siyasa. Yanzun misali in da za ka je ofishin hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi NDLEA, za ka taras ba su da isassun kayan aiki, isassu kuma lafiyayyun motocin aiki misali da makamantan su, a cikin kashi 10 misali na kayayyakin aikin da hukumar Kastelia take da shi na motocin aiki Babura da sauran kayan aiki, to hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ba ta da kashi daya daga cikin su.

Wannan shi ya sanya a halin yanzun misali, duk inda ka zaga cikin jihar Kaduna za ka ga ‘yan Kastela suna gudanar da aikinsu da isassun kayan aikin su, amma kuwa su hukumar da za su hana sha da yin tu’ammuli da miyagun kwayoyi sun yi karanci sosai, in ma ka bi diddigi sai ka taras hatta albashin da ake biyan su kila ma bai taka kara ya karya ba, ko ma ba ma a biyan su.

Idan har da gaske ana son a yi maganin wadannan matsalolin akwai bukatar a mahimmantar da irin wadannan hukumomin, kamar yanda a mataki na kasa baki-daya ne ake da hukumar NDLEA, kamata ya yi a ce kowace jiha ma tana da nata hukumar makamancin wannan, wanda muke ganin in an yi hakan za a iya samun sauki a kan matsalar gurbacewar tarbiya. Amma da yawa inda za ka tattauna da matasan za ka ji suna ce maka ai an kawo abin ne kusa da su, don haka ko da mutum ya yi tunanin ya daina sai ya ga ai ga ma wasu nan kusa da shi da wane da wane duk suna yi sai ya yi tunanin ai wannan abin ba ma wani abu ne ba, ko ma me ya yi daidai ne. hatta matsalar tsaro da ake fama da shi na masu satar mutane, fashi da makami da duk masu aikata laifuka za ka ga da yawa ana shigar masu da wannan irin miyagun kwayoyin wadanda in mutum ya sha zai ga duk abin da ya yi daidai ne, kuma zai aikata bai jin ma ya aikata laifi. Tabbas matsalar shaye-shayen nan ya yi tasiri sosan gaske wajen lalata tarbiyan al’ummarmu, musamman ma matasa, wanda a halin yanzun ma za iya cewa maza da mata kusan ma ance har ma da matan aure.

Akwai wani yanki a jihar Kano, inda na dan ga wani yanki na faifan bidiyo, in ka ga abin, abin ya yi muni abin takaici ne kwarai da gaske, yara ne kanana wanda hatta shugabansu ma bai kai shekara 16 ba, sauran duk yara ne ‘yan shekara 8 zuwa goma, kananan yara sosai a bola suke kwana. In ka ga bidiyon za ka sha mamakin wai ina hukumomi suke, ina Sarakuna suke, ina ma al’umma suke? duk inda ake yin wannan abin kuma za ka samu a cikin al’umma ne ake yi, ita kuma al’ummar ta san ba ta da nisa da inda ake yin wannan abin. In kuma har ka bar dan wani ya lalace, ko kana gani ka kyale al’umma ta lalace saboda kana ganin ba naka ba ne, zuwa gaba suna iya yin abota da nakan karshe su ma su tasirantu a kan nakan su zo suna yin irin wannan domin su ma ‘ya’yan wasu ne saboda sakaci aka kyale su suna yin irin wannan abin.

To, wannan ya taimaka sosai wajen kara yawan masu laifin wanda kuma akwai bukatar a sanya ido sosai, iyaye, hukuma, Sarakuna da Malamai ma ya kamata su sa ido sosai a kan wannan matsalar. Domin in har ba a dauki mataki ba, tabbas abin da zai rusa wannan al’ummar ta Hausawa kenan shi ne lalacewar tarbiyan yaran da ake ganin su ne za su girma su zama manyan gobe. A halin yanzun ba matasan ba, ba dattijan ba, ba iyaye matan ba. Yanzun in muka duba iyaye matan wadanda suke zama iyaye yanzun, sune fa ake sa ran su bayar da tarbiya ga al’ummar da za su taso nan gaba, to su kansu wace irin tarbiya suke da ita? In kuwa har ya kasance su iyaye matan ba su da wata cikakkiyar tarbiya, to tabbas ba za ka tsammaci wani abu mai kyau zai fito daga wannan al’umma din ba.

Za ka ga yanzun uwa ce Bahaushiya ko kuma mu ce Musulma, tana koyawa abin da ta Haifa yanda ake yin rawa, rawa ta fitsara, ko kuma yaran suna yin rawar uwar tana dauka a waya har tana turawa a kafafen sadarwa na yanar gizo ana kallo. Tana ganin abin gwaninta ne a ce diyarta ce ta yi wannan. Sabanin na da can, za ka ga uwa a kullum diyarta tun tana ‘yar shekara shida misali tana nunawa diyarta kamun kai ne da kuma wannan daidai ne wannan kuma bai dace da tarbiya ba, kar ki yi wasa da maza, kar ki yi kaza, kar ki yi kaza. Amma yanzun iyayen ne ma har suke hada gasar rawar a tsakanin ‘ya’yan na su maza da mata, iyayen suna kallo suna tafi. Wanda gaba ne ake ji, in har yaran nan suka ta so, wace irin tarbiya za su bayar? Saboda haka, in har hukuma ba ta sa ido a kan al’umma ta zama tagari ba, to kuwa tabbas akwai matsaloli masu yawa.

Exit mobile version