Connect with us

LABARAI

Maku Ya Zargi APC Na Sayan Katin Zabe A Nasarawa

Published

on

Sakataren jami’iyyar APGA ta kasa, kuma dan takarar gwamnan Jihar Nasarawa Honorabul Labaran Maku ya zargi jami’iyyar APC mai mulki da tilastawa mata sayar da katin zabe.

Ya ce; muna da tabbacin wanda a ko’ina zamu iya nunawa yadda Jami’iyya mai mulki ta APC ta nada wakilai suna bi gida-gida suna sayan katin zabe kan naira 10,000 a hannun mata da matasa.

Labaran Maku ya ce; wadanda abin ya faru dasu sune suka tabbatar mana da haka. Ya ce, wasu sun saida wasu kuma sun ki.

Ya kara da cewa APC ta talauta al’umman Jihar Nasarawa da rashin biyan albashin ma’aikata da kuma kin biyan ’yan fansho hakokinsu saboda idan lokacin zabe yayi a rika biyansu suna zaben APC.

Ya ce; yanzu talauci da yunwa ya addabi al’umma suna neman abin da za su ci shi ya sa duk abin da aka kawo wa jama’a za su yarda su sayar da katin zabe saboda su samu kudin da za su ci abinci.

Labaran Maku ya ce; Jami’iyyar APC ba za ta iya lashe zabe a shekarar 2019 ba shiyasa suke ta kame-kame suna sayan katin zabe a hannun mutane su boye .

Maku ya kara da cewa ; jami’iyyar APC ba ta yi nasara a zaben 2915 magudi aka yi yanzu sun tabbatar da al’umma ba za su zabe su ba shi ya sa suke kokarin karya karfin  al’umma ta hanyar sayan katin zabe.

Ya ce; ko da za su karbi katin zabe na hannun mata gaba daya APC ba za ta yi nasara ba, saboda al’umma sun gaji da wahala talauci yunwa da kisan kai a bayan gari saboda rashin tsaro.

Labaran Maku ya zargi Gwamna Umar Tanko Al-makura da yunkurin kashe kananan yara, ya ce; gwamnan bai san darajar ‘ya’yan Talakawa ba, ko su mutu ko su yi rai bai dame shi ba. Shiyasa ya kwashe su ya sanyasu a ginin Bene wanda babu tukuba.

Ya ce; ban da mugunta ta ya ya za a gina gidan sama babu tuku ba? Ai shi ma kansa gwamnan akwai ginin bene a gidansa me ya sa bai sanya a gina masa haka kawai daga siminti sai ya shi ba ya ce, a yi tukuba?

Ya ce; makarantar da gwamnatin Al-makura ta gina a fadin jihar duk babu tukuba ga shi makaranta bai wuce shekara uku zuwa hudu ba yana tsagewa yana faduwa.

Yanzu idan da a ce yara suna karatu haka gini zai fado a kansu su mutu kenan?

Ya roki gwamnan da ya rika yin abubuwa masu inganci saboda hakkin al’umman Jihar ne.

Labaran Maku ya ce; babu wani dan adawa da zai bani tsaro saboda na ji jama’a na ta cewa wai na janye ba zan yi takarar gwamna ba.

Ya ce; ni dan siyasa ne ina da kwarewa saboda shekarar 20 ina aiki a gwamnatin farar hula na samu kwarewa don haka babu makircin siyasa da ban sani ba.

Ya ce; ni bana siyasan addini amma ina zuwa wajen kowane addini idan aka gayyace ni.

Musulmai ne ko Kirista duk wanda ya gyya ceni zanje gurinsa saboda soyayya ya sanya aka gayyace ni, masallaci ne ko coci duk inda masoyana suka gayyace ni zan je.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: