Malam, Akwai Abin Da Ya Sauya?

Ya Kamata Malam el-Rufai ya tunawa Janar Buhari cewa, ba za a iya zabensa ba saboda tarihi ya nuna a matsayinsa na Shugaban Mulkin Soja, wanda ya kasance darasi ne ga yawancin ‘yan Nijeriya. Rashin bayar da muhimmanci ga yadda Nijeriya take a matsayinta na kasa mai mutane mabambanta.

A shekarar 1984, Buhari ya bari an shigo da akwatina guda 53 wadanda na babban dogarinshi ne ‘ADC’.

Ba tare da bin doka ba, yayi amfani da dokoki masu tsauri inda aka kashe matasa guda uku, wai don ana yaki da miyagun kwayoyi a kotun soja ba na farar hula ba.

Buhari a karkashin mulkinsa ya bai wa kansa da makusantansa kariya ta musamman daga rahoton ‘yan jarida.

Ba a manta da wannan bakar dokar ta ‘decree 4’ acce aka yi amfani da ita don kulle ‘yan jarida a wata manufa ta hana aikin jarida bakidaya a Nijeriya. Wannan bakar doka na nuna yadda ba ya bai wa hakkin mutane muhimmanci. Wannan tamkar tarihi ne ke maimaita kansa.

Exit mobile version