Malam Inuwa Waya Ya Kai Ziyarar Mubaya’a Ga Shugabancin Abdullahi Abbas A APC Kano

APC

Daga Ibrahim Muhammad,

Alhaji Inuwa Waya ya kai ziyarar taya murna da goyon baya ga Hon. Abdullahi Abbas bisa nasarar da ya samu na sake lashe zaben zama Shugaban jam’iyyar APC a karo na biyu tare da gabatar masa da bukatarsa ta shiga neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kano a shekara ta 2023.

Da yake gabatar da jawabinsa a yayin ziyarar Malam Inuwa Waya ya ce, sun je dan yin mubaya’a gare shi da yi masa murna kan zaben da aka yi masa a matsayin sabon Shugaban jam’iyyar APC da dada taya shi murna kan yadda mai girma Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya nuna shi ya sa mutane suka yarda cewa babu wanda ya cancanta ya jagoranci jam’iyyar APC fiye da shi.

Malam Inuwa Waya ya ce, “Mai girma Abdullahi Abbas yau ina shaida maka a matsayinka na babammu ni Inuwa Waya ina so in fito takara na Gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar APC a shekara 2023 kuma na san ka kai shugaba ne mai adalci mai amana da kake son ‘ya’yan ka kuma a yadda kayi shugabancin jam’iyya a baya da yanzun nan ka nuna cewa duk duk wani dan jam’iyya danka ne ka nuna babu dan mowa babu dan mowa a cikin jam’iyyar APC”, inji shi.

 

Exit mobile version