Malam Nura Sheikh Garba Maitafsiri Ya Shirya Kasaitaccen Maulidin Annabin Rahama

Shekarar Musulunci

Daga Muhammad Maitela Damaturu, 

 

A ranar Lahadi da ta gabata ce, Malam Nura na Sheikh Garba Maitafsiri Gashuwa ya gudanar da gagarumin bikin maulidi, domin murna tare da tunawa da ranar da aka haifi fiyayyen halitta, a kofar gidansa da ke unguwar Sabon Gari cikin garin Gashuwa a Jihar Yobe. Maulidi ya samu halartar dubun jama’a, maza da mata tare manyan bakin da aka gayyata ciki da wajen jihar.

 

A wani sabon salon da Malam Nura ya aiwatar a lokacin gagarumin taron wanda baya ga manyan malaman da suka albarkaci taron maulidin da jawabai masu ratsa zukata dangane da darajoji, kyawawan dabi’u tare da halayen fiyayyen halitta. Hakazalika, bikin ya kunshi bangarorin tsaro na sojoji, ‘yan sanda da jami’an tsaron al’umma (Cibil Defence), jami’an tsaron gidan yari da makamantan su, yayin da a gefe guda ga hazikai da sanannun mawakan Manzon Allah (S.A.W), wadanda suka kayata filin taron da dadadan kasidun yabo.

 

Bugu da kari kuma, taron maulidin ya samu tagomashin Malam Hafiz Abdullah Kano, daya daga cikin gwanaye kuma shahararre a fannin rera bege da yabon Manzon Allah a fadin Afrika, yana daga cikin wadanda suka gwangwaje taron da dadadan baitukan yabon Annabi, wanda shi ma mawaki Garba Na Malam Garba ya caja masoya a maulidin. A hannu guda kuma, bikin bai yi tuya ya manta da albasa ba, Malam Nura ya gayyaci gidajen yada labaru daban-daban don tafiya daidai da zamani hadi da tabbatar da sakon ya shiga kowane sako na duniya.

 

Bugu da kari, a kokarin kaucewa kowace tangardar masu kokarin aibata tarukan maulidin ta fannin dora zargin cewa da ana cakuda maza da mata a tarukan, duk da abin ba haka yake ba. Filin taron ya samu ingantaccen tsarin da ya rarraba mazaunin mata da maza daban-daban, al’amarin da ya kayatar da tafiyar da taron cikin tsanaki tare da dimbin jami’an tsoro da sauran ‘yan agajin kungiyoyin addinin musulunci, wadanda ke kokarin kyautata tsarin tafiyar da taron cikin tsanaki.

Wasu daga cikin hotunan yadda maulidin ya gudana.

Exit mobile version