Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MAKALAR YAU

…Malamai Sun Kasa Cin Jarabawar Ɗalibansu?

by Tayo Adelaja
October 29, 2017
in MAKALAR YAU
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Tare Da Musa Muhammad 08148507210   mahawayi2013@gmail.com

A duk lokacin da ake karatu, musamman na nizami irin na Boko, akwai lokutan da aka ware ana gudanar da jarabawa domin a gwada ɗalibai game da abubuwan da ake koya masu, sun gane ko kuma akasin haka, wanda kuma Malaman ne ke yi wa ɗaliban da suka koyar, kuma su Malaman ne za su duba wannan jarabawa su ba da maki.

samndaads

To, amma abin takaici sai ga shi ana samun akasin haka a wasu makarantun ƙasar nan, inda a kwanakin baya Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-rufai ya fito ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta shirya wata jarabawa ga Malaman makarantun Firamare su kimanin 33,000, inda Malamai 21,780 suka faɗi jarabawar, kuma jarabawar da suka rubuta, ta ’yan aji huɗu ne na Firamare ɗin.

Wannan jarabawa, kamar yadda gwamnatin ta bayyana, an yi ta ne don a tantance Malaman da suka san abin da duke yi da kuma waɗanda kawai albashi ne suke karɓa ba tare da aiwatar da abin da ya kamata su yi ba. Domin maƙasudin jarabawar shi ne a gane kaifin hazaƙa da fahimtar da Malaman makarantun ke da ita a Jihar ta Kaduna.

Har a cikin jawabin nasa, Gwamna El-rufai ya ce, “mun shirya wa Malaman makarantun Firamare su 33,000 jarabawa irin wacce ake yi wa yara ’yan aji huɗu a Firamare. A jarabawar sai muka tsara cewa, waɗanda suka samu aƙalla kashi 70 cikin 100 ne suka ci, amma abin baƙin ciki, kashi 66 cikin 100 daga cikinsu sun faɗi jarabawar.”

Lokacin da na ji wannan labari hankalina ya tashi, musamman a matsayina na ɗan jihar Kaduna, kuma wanda ya yi makarantar gwamnati tun daga Firamare har Sakandare. Tunanina ya komawa ga cewa yanzu abin har ya kai ga haka ne. Idan yau aka ce Malami ya kasa cin jarabawar da ya kamata ya yi wa ɗalibansa, ya abin yake ke nan?

Don ganin ya kare kansa daga wannan abin kunya, Gwamna El-rufai ya bayyana cewa a shekarun baya an mayar da batun ɗaukar Malamai abin siyasa, an kwashi waɗanda ba su cancanta ba, shi ya sa su suka ɗauki mataki na kai canji a al’amarin, inda za su kawo ƙwararrun Malamai matasa, domin su gyara ɓangaren a duk faɗin jihar.

Sannan kuma daga cikin matakan da yake ganin za a kawo ƙarshen wannan abu, shi ne za a yi canje-canjen Malamai daga wannan gari zuwa wancan saboda a kawo daidaituwar al’amura, kamar dai yadda muka san ana yi a zamanin da.

Duk da Gwamnan ya ɗora laifin wannan abin kunya ga gwamnatocin da suka gabata, inda ya yake zargin ba a bin ƙa’aida wajen ɗaukar Malaman, su ma a nasu zamanin ba a ga me suka yi don ganin sun shawo kan wannan matsala ba, domin yanzu a kusan shekaru sama da biyun da suk akwashe akan mulki, ba a ji wannan abu ba sai yanzu.

Lallai kam akwai wannan zargi, kuma wannan ya zama abin da ya wajaba a bi duk hanyoyin da za a bi don ganin magance wannan abin takaici. Domin idan aka duba, za a ga cewa an mayar da ɗaukar Malaman Firamre tamkar siyasa, sai mai uwa a murhu ne kawai suke samu ake ɗaukarsu, ba tare da la’akari da ko sun san abin da suke yi ko ba su sani ba, ba tare da ko suna da ƙwarewa ko babu ba.

Wannan abu na rsahin ƙwararru a makarantu, musamman na Firamare, ba a jihar Kaduna ne kawai yake ba, idan da a ce su ma sauran jihohi za su yi koyi da na Kaduna, wata kila ma a wasu jihohin sai an samu inda ya fi na Kaduna muni. Haka kuma ba za a rasa samun irin wannan matsalar a sauran harkar ilimin ba, musamman a makarantun Sakandare.

Akwai wata jiha a cikin jihohin Arewacin ƙasar nan da Gwamnan ya yi ƙoƙarin ganin an tantance masu ilimi da takardun jarabawa na gaskiya, ba wai takardun jabu ba, inda a ƙarshe ya zama aka samu cewa yawancin Malaman da ke koyarwa tantiran jahilai ne na ƙin ƙarawa, kamar dai na jihar Kaduna, sai dai su waɗannan makarantun Sakandare ne.

Lalacewar harkar ilimi a ƙasar nan ta shafi kusan kowane fanni na harkar, wanda idan ba da gaske gwamnati ta yi ba, abin ka iya zama wani abin kunya ga ƙasa, balla ’yan ƙasar. Domin ko a Jami’o’i da makarantun gaba da Sakandare, abin yana da muni, ta yadda a wasu lokutan ma ɗalibai ke sayen jarabawa, mata kuma a rinƙa amfani da su don a ba su maki.

Irin waɗannan abubuwa da ke faruwa a makarantunmu, tun daga Firamnare har Jami’o’i, abubuwa ne da suke a bayyane, kamar dai yadda Gwamna El-rufai ya fasa ƙwai. Domin a kwanakin baya ƙungiyar Malaman Kwalejin koyon aikin gona ta jihar Bauchi (ASUP) ta fallasa wata mummunar harƙalla, wacce suka zargi Shugabanin Kwalejin na gudanarwa wajen ba da shaidar kammala karatu ga waɗanda ba su dace ba.

Ƙungiyar ta yi zargin cewa ana amsar na goro domin ba da shaidar kammala karatu a Kwalejin ga waɗanda ba su cancanta ba, da kuma ba da takardar shaidar kammala karatu na jabu ga wasu ɗaliban da aka samu takardun a hannunsu.

Wannan zargin fa ya fito ne daga bakin Shugaban ƙungiyar ta ASUP, Kwamared Ahmed Mohammed Bununu a wani taron manema labarai da ya gabatar a Bauchi kwanakin baya, har ma yake cewa akwai wani ɗalibi a matakin babbar Diploma ta HND II, wanda aka ba shi izinin karatu da zimmar kafin ya kammala zai kawo shaidar sauran darussan da ya faɗi a Sakandare, amma abin mamaki aka ba shi shaidar kammala karatun ba tare da kawo wannan bashin ba.

Dduk dai a wannan Kwalejin, ƙungiya Malaman ta yi zargin cewa an kama wani ɗalibin Diploma da satar amsa a yayin jaraba, amma ya samu shaidar kammala karatunsa, duk da kuwa dokar Kwalejin ta gindaya kora ce ta rataya a gareshi.

Sai dai alhamdu lillahi, Shugaban ƙungiyar Malaman ya tabbatar wa da al’umma cewa, “a matsayinmu na ƙungiya ba za mu taɓa yin barci mu zura ido ana cin hanci da rashawa a cikin kwalejin ba, ba kuma za mu lamunci dukkan gurɓatattun halaye da ke wakana a cikin wannan Kwalejin ba, za mu tashi tsaye domin kare martabar wannan Kwalejin a kowane lokaci.”

Na kawo wannan misali ne don a gane cewa lalacewar harkar nan mai muhimmanci ta ilimi, daga sama ne har ƙasa, wanda kuma, kamar yadda na faɗa a sama, idan ba wani huɓɓasa Hukumomi suka yi ba, abin zai iya zama wani abin kunya da haɗari ga ci gaban ƙasar nan.

SendShareTweetShare
Previous Post

Sharhin Serie A: Waye Zai Iya Tsayar Da Juventus A Ƙasar Italiya?

Next Post

Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya

RelatedPosts

Sulhu Da ‘Yan Bindiga: Me Ya Sa Sheikh Gumi Na Tufka Wasu Na Warwara?

Sulhu Da ‘Yan Bindiga: Me Ya Sa Sheikh Gumi Na Tufka Wasu Na Warwara?

by Sulaiman Ibrahim
6 hours ago
0

Ni da ma tun da farko ban taba tunani ko...

Rance

Kura-kuren Da Hukumomi Ke Yi Wajen Bayar Da Rance

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Aliyu M. Kurfi (PhD), Ya kamata mu sani cewa...

Ilimi

Satar Dalibai Ko  Kassara Ilimi A Arewa?

by Muhammad
4 days ago
0

alimailafiyasunusi@gmail.com - 08036064695: A yanzu babu abinda ya fi jan...

Next Post

Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version