Bello Hamza" />

Malamai Sun Nemi Gwamnatin Kano Ta Bude Makarantun Islamiya

Wasu gungun Malamai a karkashin jaroancin Sheikh Sabiu Abdulsalam, sun bukaci gwamnatin jihar Kano ta sake bude makarantu islamiyoyin jihar da aka kulle sakamakon bullar cutar korona don su cigaba da harkokinsu na bayar da ilimi.

Sheikh Abdulsalam ya yi wannan kiran ne a hudubarsa ta sallar juma’a a masallacin Namadina da ke Darmanawa, Kano.

Ya ce, cigaba da kulle makarantun da aka yi a wata Afrilu sakamakon bullar cutar korona yana cutar da al’umma.

”Muna kira ga gwamnatin jihar Kano da ta sake buce makarantun a ta kulle sakamamon bullar cutar korona don kullewarsu na cutar da al’umma gaba daya.

“Cigaba da kulle makarantun ya haifar da matsaloli daban daban wanda yara da yawa suka fada saboda rashin zuwa makaranta.

”Tabbas lokaci ya yi sa za a sake bude makarantu don yara su cigaba da karatu,” inji shi.

Ya kuma kara da cewa, tun da gwamnati ta sake bude kasuwanni ba wuraren kallon kwallon kafa da sauran wuraren shakatawa, to babu wani dalili na cigaba da kulle makarantun mu.

”Ba mun karyata kasancewar cutar korona ba ne amma tun da aka bar wasu wuraren shakata su cigaba da harkokinsu ya kamata  a bar makarantu su ma su cigaba da bayar da karatu,” inji shi.

Malamin ya ce, addinin musulunci ya mahimmantar da neman ilimi saboda haka bai kamata a dauke shi da wasa.

Exit mobile version