Aliyu Nadabo" />

Malaman Firamare 3,500 A Ka Horas Don Koyar Da Dalibai Ta Hanyar Wake

Kebbi

Kimanin malaman makarantun firamare 3500 aka horars kan sabuwar hanyar ba da ilimi ta hanyar wake ga dalibai ‘yan aji daya a fadin jihar Kaduna.

Malam Dahuru Anchau, mataimakin Darakta mai kula da makarantu masu zaman kansu, karkashin maaikatar Ilimi, kimiyya da Fasaha ta jihar Kaduna, ya sanar da haka yayin da yake zagayen gani da ido a makarantar Malam Jalo da ke Rigachukun jihar Kaduna, a makon da ya gabata.

Ya kuma ce, malaman jimilarsu dubu uku da dari biyar  kuma an zakulo su ne daga makarantu daban -daban a fadin jihar Kaduna, wanda suka samu horas wa kan yadda za su inganta koyar da dalibai yan aji daya na makarantun Framare a fadin jihar Kaduna

Dahuru ya bayyana cewa kimanin Naira Biliyan Shida  aka ware don samar da kayan aiki da horas da malamai wanda ke karkashin wata hukuma mai suna Global Partnership for Education (GPE)

Ya kara da cewa kudin wanda aka kasafta shi don tafiyar da karatun cikin Shekara hudu, Wanda acewarsa ana zangon shekara uku a cikin shirin

Da take tsokaci a kan shirin, Shugaban Makarantar Mal Jalo Model, Rigachukun, Malama Asabe Danlami ta sanar cewa kashi Saba’in daga cikin Dari na Daliban aji Daya na  Framare Sun iya karatu da rubutu ta hanyar wake

Ta kara da cewa wannan sabon  tsarin karatun ya ciyar da ilimi gaba a fadin jihar ta Kaduna ta yadda dalibai yan aji daya kan iya hada kalmomi da karantasu ta hanyar wake da rawa

A don haka ta yaba hukumar Ilimi karkashin  Gwamnatin Jihar Kaduna don irin namijin kokari da takeyi don ciyar da ilimi gaba

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, wani Dalibi dan Aji Daya mai suna Muhammad Abdullahi dake Makarantar Mal Jalo Model Framare da ke Rigachukun a jihar Kaduna, ya sanar cewa ya iya hada kalmomi da karantawa ta hanyar wake

Ya bayyana cewa wannan tsarin karatun ya basu dama ta yadda kusan dukkan abokan karatunsa sun iya hada baki da karantawa

Abdullahi ya jinjinawa malamansu irin jajircewa da sukayi da bada lokacinsu wajen tabbatar da daliban sun iya hada kalmomi da karatu.

Da take nata tsokacin Hajiya Halima Jumare Babba Darakta a Maaikatar Ilimi, kimiyya da fasaha ta jihar Kaduna , Hajiya Halima Jumare ta sanar cewa tsarin ya yi  tasiri matuka,  kuma ya habaka hanyar koyarwa a makarantu

Ta kara da cewa dalibai yan aji daya na daukar karatu da sauri, tan kara da cewa sun iya hada kalmomi da karantawa ta wannan sabon tsarin

Jumare ta yabawa Gwamnatin Jihar Kaduna, karkashin Gwamna Nasiru Ahmed El-Rufa’i ta yadda  ya ba Ilimi mahimmacin gaske a fadin jihar Kaduna.

Exit mobile version