Malaman Jami’a Sun Dakatar Da Yajin Aiki Bayan Wata Tara

Jami'a

Daga Mahdi M. Muhammad,

 

Kungiyar Malaman jami’o’in a Nijeriya (ASUU) ta dakatar da yajin aikin da ta kwashe tara ta na yi, wanda ya kawo cikas ga harkokin ilimi a kasar.

Yayin da ya ke jawabi a taron manema labarai da safiyar Laraba a jami’ar Abuja, shugaban ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya bayyana cewa, an yanke shawarar komawa ajin aikin ne bisa la’akari da yarjejeniyar da aka cimma da gwamnatin tarayya a taron da aka gudanar a ranar Talata, wanda aka tattauna a kan mafi yawan bukatun kungiyar.

Ya ce, an kafa kwamitin aiwatarwa da za ta sanya ido kan aiwatar da yarjejeniyar.

“A bisa abin da ya gabata ne NEC ta yanke shawarar cewa yajin aikin da kungiyar ke yi a halin yanzu ya kamata a dakatar da shi bisa sharadin fara aiki daga 12.01 na safiyar Alhamis, 24 ga Disamba, 2020. Amma, idan har gwamnati ta kasa cika nata bangaren na yarjejeniyar, ASUU za ta ci gaba da yajin aikin da ta dakatar kamar yadda ake ganin ya cancanta,”in ji shi.

Yajin aikin ASUU ya fara ne a ranar 23 ga Maris bayan yajin aikin gargadi na mako biyu da ya kare ba tare da warware rikicinsu da gwamnati ba.

Rufe jami’o’in da yajin aikin da bai taka kara ya karya ba ya sanya gwamnati kara rufe makarantu sakamakon barkewar cutar korona.

Daliban jami’o’in mallakin gwamnatin Nijeriya sun yi asara karatun su gaba daya na shekarar saboda dogon rikicin da ke tsakanin gwamnati da malamai.

Shugaban kungiyar ASUU wanda ya bayyana wasu shawarwari da kungiyar ta ASUU NEC ta cimma a taron ta da suka gudanar a daren ranar Talata don nazarin rahotannin yarjejeniya da gwamnatin tarayya, ya ce, kungiyar ta yanke shawarar ba wa gwamnatin tarayya wata dama don tabbatar da cewa za a iya amincewa da ita.

Ya ce, NEC ta amince da amincewa da yarjeniyoyin da ASUU da gwamnatin tarayya suka cimma a ranar Talatar Disamba, 2020 kuma ta yanke shawarar sanya ido da kuma himma wajen sanya ido kan aiwatar da ita.

Da aka tambaye shi ko gwamnatin tarayya ta iya cika alkawarinta na fara biyan basussukan albashin mambobin ASUU, Ogunyemi ya ce, ta fara duk da cewa ba ta kammala ba tukunna.

Ogunyemi ya ci gaba da cewa, an kuma amince cewa babu wani mamban ASUU da zai yi asarar duk wata alfarma da ya cancanta sakamakon shiga yajin aikin. Kungiyar ta yanke shawarar bin bangarorin a yarjejeniyar ta da gwamnati a shekarar 2009 da ‘Memoradum of Action 2013’ wadanda ke bukatar doka kamar su sanya alawus din Ilimin da aka Samu (EAA) a cikin kasafin kudin shekara-shekara da kuma kwaskwarimar dokar zartarwa a girmama dokar hukumar jami’ar kasa (NUC) ta 2004.

“Kuma a karshe, NEC ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin da aka fara a ranar 23 ga Maris, 2020, wanda zai fara daga 12.01 na safiyar Alhamis, 24 ga Disamba, 2020,” in ji shi.

Exit mobile version