Kungiyar Malaman jami’o’in gwamnati na Nijeriya (ASUU) sun fara wani yajin aikin daga ranar Lahadi 13 ga watan Agusta.
A cewar kungiyar malaman jami’ar sun bayyana wannan matakin nasu ne bayan taron kungiyarsu ta, ASUU, da safiyar yau Litinin.
A yayin ganawar kungiyar, shugaban kungiyar ASUU, Biodon Ogunyemi ya bayyana dalilansu na fara yajin aikin, inda yace, Malaman na neman a biya musu wasu bukatu da suka hada da al’amuran jin dadin malamai, da karin kudaden gudanarwa domin inganta yanayin ilimi a jami’o’in Kasar.
Kungiyar ta ASUU ta kara da cewa, malamai da dama daga jami’o’in dake wasu sassan kasar basa samun cikakken albashinsu kamar yadda ya kamata.