Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home ADON GARI

Malaman Makaranta Mu Kara Hakuri Wurin Tarbiyyar Dalibai – Fatima Alhassan    

by Muhammad
February 19, 2021
in ADON GARI
4 min read
Fatima
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

FATIMA ALHASSAN, hazikar Malamar makaranta, ta shawarci abokan aikinta Malaman makaranta da su daure su kara hakuri wurin ci gaba da tarbiyyar daliba. Malama Fatima ta yi wannan kira a cikin hirarta da ADON GARI. Ga yadda hirar ta kasance: 

 

samndaads

Da farko masu karatu za su so suji cikakken sunanki da sunan da aka fi saninki da shi?

 

 

Ko za ki ba wa masu karatu tarihinki a takaitace?

Eh toh ni dai an haife ni ne a cikin garin Bauchi ranar 5 ga Agusta 1980, na yi makarantar Firamare na a ‘Federal Gobt Girls college staff school daga 1986 zuwa 1991 na shiga Sakandare a nan FGGC Bauchi daga 1991 zuwa 1997 na kuma wuce Jami’ar Maiduguri don karin ilimi, kuma  na gama a 2005 da BA (Bachelor of Arts) English Literature, a 2009 Kuma na yi PGDE.

 

 

Me ya ja hankalinki kika zabi fannin Ilimi?

 

 

 

Wacce irin matsala ce a bangaren ilimi ta fi addabar mutane?

Gaskiya yin ko oho da ilimi ta bangaren iyayen da yaran musamman ta nan Arewacin Nijeriya da ilimin boko ya kasa duk da cewar ma makarantan kyauta ce amma za ka ga yara na yawo cikin gari kuma iyaye ba su ce komai ba musamman yara mata.

 

 

Wadanne hanyoyi  Ma’aikatan ilimi da kuma gwamnati ya kamata su bi domin ganin an magance wannan matsala?

 

Gwamnati ta sa doka ga iyayen da za’a a samu ‘ya’yansu na yawo lokacin makaranta. Masu unguwanni su ma saka Ido don ganin cewa an maganci wannan matsalar.

 

 

 

 

 

 

 

Wace rawa jama’a za su taka don ganin ilimi ya ginu a cikin al’umma?

To su yi kokarin kai ‘ya’yansu makaranta a kan lokaci kar yaro sai ya kai shekara 12 ka ga iyaye na kawo shi wai a sa shi a aji daya alhali ‘yan ajin kananane ‘yan shekara shida zuwa bakwai.

 

 

Wane kira za ki ga iyaye da Malamai A kan ‘ya’yansu?

A gaskiya kiran da zan yi wa iyaye da Malamai shi ne mu samu lokacin yaran nan a gida da makaranta mu yi kokarin taimakawa wajen ganin yaran nan su cimma burin su. kuma mu kyautata muamalarmu da su.

 

 

 

Akwai mata da yawa masu sha’awar irin wannan aiki naki na bangaren ilimi, wacce irin shawara zaki basu don ganin sun cimma burinsu?.

 

Ai harkar koyarwa a kan ce ta mata ce, daman ana so su zage dantse kawai a je makaranta a yi karatu a nemi aikin koyarwar.

 

 

 

 

Zaki ga wasu mazan suna da matan da su kai karatu irin naki, amma kuma sun gagara barinsu su yi aiki, wanne irin kira zaki wajen ganin sun bar matansu ko ‘ya’yan su sun yi irin wannan aiki?.

 

To gaskiya maza ku yi kokarin barin matanku da su yi aiki don shi ne aikin da mace za ta yi, kuma ta dawo gida tare da ‘ya’yanta ba tare da wata matsala ba don taimakekeniya a fannin ilimi ma na da kyau a addinance, to ba dai dai bane a killace ta da iliminta.

 

 

 

 

Wanne irin kalubale kika taba fuskanta a bangaren aikinki?

Mhm, zagi daga iyaye musamman iyaye maza tun ba a ce karfe 7:45 na safe ta yi kuma na kulle kofar makaranta ba, ki ji zagi wani har da cewa, ni mace ban kai ya roke ni ba kuma a gaban yaran fa da dai sauran.

 

 

 

 

Menene burinki na gaba game da aikin ki?

 

Burina a gaba shi ne in daura a inda na tsaya a karatu sai in nemi koyarwa a Jami’a don ba wa ‘yan baya wuri su taba suma su daura damarar koyarwa mukamin in sha Allahu.

 

 

 

Wanne irin kira zaki ga sauran ma’aikatan ilimi?

 

Kira na shi ne mu cigaba da hakuri da yaran don Amana ce a garemu, kuma Malamai mu daina zaman karkashin bishiya.

 

 

 

Me zaki ce da Jaridar LEADERSHIP A Yau Juma’a?.

Jaridar LEADERSHIP A Yau, Juma’a aikin ku na kyau don na karanta na mutane da byawa kuma ina jin dadin yadda kuke kokarin ciyar da al’amura gaba.

 

 

   Muna godiya da bamu lokacin ki da kika yi.

SendShareTweetShare
Previous Post

Muhimmancin Yarda Da Juna A Tsakanin Ma’aurata

Next Post

Fasahar Sarrafa Takardar Lian-shi-zhi Mai Dogon Tarihi A Kasar Sin

RelatedPosts

Mata Kada Mu Raina Sana’a Komai Kankantarta – Zuwaira Bako

Mata Kada Mu Raina Sana’a Komai Kankantarta – Zuwaira Bako

by Sulaiman Ibrahim
2 weeks ago
0

Zuwaira Mohammed Bako ‘yar boko, ma’aikaciyar gwamnati, sannan kuma ‘yar...

Nemi

Duk Kudin Miji Ki Kar Ki Sa Ran Naki Ne, Tashi Ki Nemi Nakanki – Khadija Mahmoud

by Muhammad
3 weeks ago
0

Sana’a a wannan zamanin ita ce abar dogaro ga matan...

Shawarata Ga Mace Ki Yi Kokari Ki Dogara Da Kanki Kafin Ki Yi Aure – Maryam

Shawarata Ga Mace Ki Yi Kokari Ki Dogara Da Kanki Kafin Ki Yi Aure – Maryam

by Sulaiman Ibrahim
4 weeks ago
0

Ba na iya shiru in kyale Matan da su ke...

Next Post
Takardar

Fasahar Sarrafa Takardar Lian-shi-zhi Mai Dogon Tarihi A Kasar Sin

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version