Daga Abubakar Abba, Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna Ahmed Nasir El-rufai ya bayyana cewa, malaman makarantar Firamare ta gwamnati su 50 da gwamnatin ta taso domin ta kara mayar da su aiki sun gaza cin jarrabawar aji hudu na Firamare.
Ya ce, wannan ita ce ka’idar da aka gindaya wa malaman in sun ci jarrabawar za a mayar da su kan aikin, amma suka gaza ci.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin wani taro da yayi da sarakunan gargajiya dake Kudancin jihar, lokacin da suka kai masa ziyara jiya a fadar gwamnatin jihar.