Malaman Makarantar Firamare A Kaduna Sun Kasa Cin Jarabawar ‘Yan Aji Hudu

Daga Abubakar Abba, Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Ahmed Nasir El-rufai ya bayyana cewa, malaman makarantar Firamare ta gwamnati su 50 da gwamnatin ta taso domin ta kara mayar da su aiki sun gaza cin jarrabawar aji hudu na Firamare.

Ya ce, wannan ita ce ka’idar da aka gindaya wa malaman in sun ci jarrabawar za a mayar da su kan aikin, amma suka gaza ci.

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin wani taro da yayi da sarakunan gargajiya dake Kudancin jihar, lokacin da suka kai masa ziyara jiya a fadar gwamnatin jihar.

Akan daliban makarantun Sakandare da gwamnatin ta dauki nauyinsu don karo karatu a kasar waje. El-rufai ya ce, gwamnati ta dawo dasu gida, saboda sun kasa yin wani abin azo a gani makarantun da aka tura su.

Exit mobile version