Malaman Tijjaniyya Na Kano Sun Kai Wa Kalifa Muhammad Sanusi ll Ziyarar Mubaya’a

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Majalisar Shura ta Darikar Tijjaniyya ta Jihar Kano ta kai wa Maimartaba Sarkin Kano na 14 Malam Muhammadu Sanusi II ziyarar mubaya’a bisa nadin da aka yi masa na babban Khalifan Shehu Ibrahim Inyass a Nigeria.

Malaman sun yi wa Malam Muhammadu Sanusi ll mubaya’ar ne ranar Asabar karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Awaisu Limanci.

Malaman da suka kai ziyarar mubaya’ar sun hada da Khalifa Tuhami Shehu Atiku da Shehi Shehu Maihula da Imam Muhammad Nura Arzai da kuma Sheikh dayyabu dan Almajiri.

Sauran sun hada da Khalifa Hassan Sani Kafinga da Khalifa Bashir Musa Kalla da Khalifa Fatihi Uba Safiyanu da Khalifa Kamilu Yalo da Sheikh Tijjani Maisalati Indabawa da kuma Sheikh Kabiru Zango.

Tawagar kuma ta kunshi zuriyar Shehu Ibrahim Inyas mazauna Kano karkashin jagorancin Sayyada Rahama Ibrahim Inyas.

Exit mobile version