Connect with us

RA'AYI

Malami: Shugaban Sashen Shari’a Mai Hankoron Kare Martabar Nijeriya

Published

on

Dokoki na kwarai sune tubalin samar da zaman lafiya a kasa. Idan aka samu mutane marasa nagarta suka samar da dokoki ba zai wani haifar da natija ba, amma idan mutanen kwarai suka samar da dokoki sai ka ga an samu ci gaba a al’umma.

Kwarewar mai tabbatar da doka a kasa shi ne ya zama cikakken dan kishin ksa. A matsayinsa n Babban Lauyan da ya samu tambarin SAN, Babban Lauyan Nijeriya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya nuna kwarewa a tsarin gudanar da ayyukansa. Aikin Babban Lauyan Gwamnati shi ne ya shigar da karar ko wane ne a gaban kotu a madadin gwamnati.

Fiye da lokutan baya a tarihin Nijeriya, Babban Lauyan Gwamnagti Abubakar Malami ya na matukar kiyaye hurumin ‘yan kasa, kiyaye darajar bangaren shari’a a yayin gudanar da aikinsa.

Wani babban aiki da aka shaidi Malami da shi, shi ne batun bibiya da dawo da kudaden Nijeriya da aka sace aka kai wasu kasashen. Ya taimakawa gwamnati wurin kwato kudaden sata a ciki da wajen Nijeriya. Kadan daga ciki shi ne samun nasarar dawo da Dala Miliyan 311 wanda Sani Abacha ya sata ya kai Amurka.

Makiya a ciki da wajen Nijeriya sun yi ta kokarin kawo cikas ga tsarin dawo da wadannan kudaden sata, amma salon Malami shi ne yin buris da wadannan baragubi, wannan ne kuma ke kunyata su yayin da Nijeriya ke ci gaba da amfana. Saboda kwarewar Malami, Nijeriya ba ta bukatar neman tallafi daga wani ko wasu kafin ta kwato kudadenta.

A karkashinsa, a yanzu a Nijeriya babu wani da aka kulle ba tare da shari’a ba. A baya kuwa sai ka tarad da mutane an kulle su haka nan ba tare da an kai su kotu ba. Tarihin da gwamnatin Buhari ta kafa a fannin yin tsaftatacciyar shari’a tana da alaka da irin rikon da Babban Mai Lauyan Gwamnati, Malami ya yi wa ofishinsa. A yanzu ne muke ganin bangaren shari’a wanda ke gudanar da komi bisa doka ba son ran wasu tsiraru ba.

A yayin da lamarin fyade ya ta’azzara, Babban Lauyan Gwamnati Malami, ya bayar da tabbacin cewa gwamnati na yin wani shiri domin samar da kotuna na musamman domin fuskantar lamarin. Sanin kowa ne yanzu lamarin na fyade ya wuce kima, don BAbban Sufeton ‘Yan Sanda ma ya ce a watanni bakwai an samu kyasa-kyasai 717 na fyade.

Haka nan kuma a yunkurin gwamnati na dakile rashawa a tsakankanin ma’aikatan gwamnati, Nijeriya na ci gaba da ganin natija a karkashin Malami. Daya daga cikin wannan kuwa akwai batun bayar da ‘yancin cin gashin kai ga Majalisun jihohi da bangaren shari’a. Malami ya tabbatar da cewa babu wani tursasawa ko turjiya da zai hana gwamnati tabbatar da wannan lamari.

Shi babban burinsa shi ne yin abubuwan da za su tsamo Nijeriya daga halin da gwmanatocin baya suka jefa ta. Shi ba ya tsoron fuskantar abu matukar ya san akan gaskiyarsa yake. Misali, ya gargadi yan Nijeriya da ke da kadarori a wasu kasashe da su rika biyan haraji, sannan kuma duk wani banki da aka kama yana taimakawa wani dan Nijeriya wurin boye kadara a waje, zai janyo a ci taran bankin.

Saboda irin halin da duniya ta tsinci kanta na damuwar Korona, sai ya mayar da hankalinsa kan ci gaban fasaha na zaman, inda ya ce kotu na iya zama ta intanet.

Malami jajirtacce kuma tsayayyen mabiyi Buhari ne. Idan za mu waiwayi tarihi za mu ga cewa shi ne lauyan Buhari a CPC. Duk da ba wai wannan ba ne kawai ‘yar manuniya ga biyayyansa ga Buhari.

Ya tsaya tsayin daka tare da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bayan zaben shekarar 2011, inda aka yi ta fafata shari’a da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan.

A yayin da manyan lauyoyin Nijeriya ke kaucewa goyon bayan Buhari a kotu, manyan lauyoyi uku ne kawai suka tsaya mishi a kotu, Malami, Oladipo Okpeseyi da kuma marigayi James Ocholi. A lokacin Okpeseyi ne shugaban tawagar lauyoyin.

Duk da Malami ya fuskanci kalubale daga ‘yan adawa tun bayan da aka ayyana shi a matsayin Babban Lauyan Gwamnati, wannan bai hana shi mayar da hankali kan aikinsa ba. Su burinsu kawai da wani dan amshin shatansu aka zabo aka ba wannan mukami ba malami ba. Shi ne dalilin hayaniya da farfagandarsu.

Shi Shugaba Buhari ya san me ya sa ya dauko Malami. Kuma ma dai wanne laifi Buharin ya aikata don ya dauko mutumin da ke da kwarewa wanda an shaidi aikinsa a shari’ar zaben shugaban kasa ta shekarar 2011? Su ba damuwarsu kwarewa ko iya aikin Malami ba, damuwarsu ita ce yadda ya toshe duk wata kafa da za a iya yin rashin gaskiya ko a cutar da Nijeriya. Aiki kawai ya sa a gaba, don ganin ya ceto Nijeriya. Kuma karin haushin da suke da shi shi ne yadda ya dakile batun rashawa. Idonsa na nan a ko ina yana kallon yadda ake tafiyar da lamurra.

Na yi imanin cewa idan a yau babu Malami a ofis, wanda shi ne burinsu, za su daina batunsa ne su dira kan wanda ya maye gurbinsa matukar ba nasu ba ne. Sai dai abin takaici gare su shi ne babu wata alama daga Shugaban Kasa na sauya mukarrabansa, balle su yi mafarkin za a cire Malami.

– Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da Tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa (Presidential Support Committee)

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: