Malamin Makaranta Ya Shekara Hudu Ya Na Yi Wa ’Yarsa Fyade A Legas

An kama wani mai suna Segun Durojaiye dan shekara 52 malami a makarantar Ijagba da ke Sotubo a garin Sagamu da laifin yi wa ‘yarsa ‘yar shekara 16 fyade har na tsawon shekara 4, an kama mutumoin ne da dan uwansa Emmanuel Durojaiye, yarinyar na zaune da mahaifin nata ne a layin Baba-Benja da ke unguwar Oreyo a Igbogbo Ikorodu ta jihar Legas.

Majiyar ta shaida mana cewa Segun ya karbi kulawa da yarinyar ne bayan rasuwar mahifiyar ta in da shi da kishiyar uwar suka ci gaba da renon yarinyar har zuwa shekarar 2014 lokacin da kishiyar uwar ta rasu daga nan ne ta koma Abuja wajen wani danuwansu. Bayan ‘yan watanni ne Segun ya umurci da ta dawo gida in da ya ci gaba da jima’i da ita yana mai yi mata barazanar ka da ta gaya wa kowa.

Bayani ya nuna cewa, ana cikin wannan hali ne wata rana ta ziyarci kanin mahaifin ta Emmanuel dan shekara 42 in da shi ma ya yi mata fyade daga nan ne su biyu suka ci gaba da jima’i da ita ba kakkauta wa.

Wakilinmu ya gano cewa, wani lokaci a watan Disamba 2107 yarinyar ta yi karfin halin bayyana wa wata ‘yaruwarsu in da ita kuma ta yi wa kakarsu bayanin halin da ake ciki.

“Kakar ta yi kokarin boye maganan amma da wasu makabta suka ji labarin sai suka nemi lauya ya rubuta takardar koke a madadin yarinyar zuwa kwamishinan ‘yansanda in da a ka kama mahaifin nata da kawun ta, “Anu kuma su muka tura “Case” din sashin bincike na farin kaya da ke Yaba”

“Tuni suka amsa laifisu in da suka tabbatar da yin jima’i da yarinyar sau uku-uku, daya daga cikin ‘ya’yan Segun ya bayar da karin shaidar cewa, lallai ta gaya masa mahaifinsu na jima’i da ita ya kuma gargade shi akan lallai ya bari”

Majiyar namu ya shaida mana cewar yarinyar ta gaya wa ‘yan sanda cewa sau biyu mahaifin nata na yi mata ciki, kawun ta kuma sau daya ya yi mata, su kan kai ta wani wuri ne a zubar da cikin. “Ta ce mahaifinta ya fara jima’i da ita ne tun tana shekara 13 a duniya kuma sau uku ana zubar mata da ciki”

Jami’in hurda da jama’a na hukumar ‘yansanda jihar Legas Chike Oti ya tabbatar da faruwar lamarin, “Mun samu labarin abin da ya faru ne ta hanyar takardar koke da wani lauya ya rubuta mana, tuni kwaminshinan ‘yansanda Edgal Imohimi ya bayar da umurnin sashin SCIID ya ci gaba da bincike”

‘Kwamishinan ‘yansanda a shiye ya ke domin hada hannu da hukumomin gwamnati wajen tabbatar da hakkin yara da kare su daga miyagu masu bata rayuwarsu, zamu tabbatar da an hukunta duk wanda muka kama da kaifin yin lalata da yara kanana” in ji shi.

An gurfanar da masu lafin a gaban kotun majastare da ke Yaba in aka tuhume su da laifi 8 da suka hada da fyade da zubar da ciki.

Bayan karanta musu laifuffukansu a karkashi dokokin jihar Legas sashi na 145(2) sun musanta aikata laifin, daga nan ne alkali Oluwatoyin Oghre ya bayar da belinsu a bisa sharadin tsayawar mutum biyu a kan kudi Naira Miliyan 1, dole masu tsaya musu su kai matakin albashi 15 a aikin gwamnati ko kuma mai rike da sarautar gargajiya tare da shaidar cikakken biyan haraji, an dai daga shari’a zuwa ranar 12 ga watan Maris 2018.

Exit mobile version