Connect with us

ADABI

Mallam Bahaushe Ga Naka (II)

Published

on

Kashegari, Halisa da kanwarta Turai su ka kwashe wuni guda katakar su na hirar dabi’o’in Atika mai tuwo, ita da yaranta da mijinta Baballe direba. Cewa shekarar su uku tare a wannan unguwa amma ba su san mijinta ba, ya na can yawon dandi. Da farko sai da ya shekara guda a Ibbo. An sa malamai sun yi masa kiranye, amma a banza, wai man kare. Ya bar mata ‘ya’ya maza da mata, ga su duk sun girma, wasu ma sun isa aure. Ya jefa su cikin halin talauci da babu, halin sagada-sagada, wai auren bashi, cewar masu azancin Hausa, ‘tun ba a biya bashin ba mata ta haihu’. Ga wannan zamani mawuyaci da ake ciki, na galiban sai ka ga talaka ya rasa aikin yi ko hanyar samun abinci. Wannan ya sanya yaran, kowa ya kama gabansa.

To sai Turai ta shiga bincike, jin cewa Baballe makwabcinsu ya shekara uku ba ya a gida. Ta gyara zama ta nemi ta ji dalili. Ta dokanta, ta zaku ta ji tarihinsa ma da kuma dalilin barinsa gida, har ya gudu daga iyalansa. Halisa ta yi mata nuni da cewa ita ce babbar aminiyar Atika, cewa duk unguwar ba matar da ta ke shiri da ita sai ita. Don kuwa su na iya kwashe wuni guda a gidanta su na hira; ta na ba ta labarin halin da Duniya da jama’ar da ke cikinta su ke. ‘Ni na san tarihinta ciki da bai, ina ma iya rubuta littafi a game da ita’, cewar Halisa. Halisa ta fara ba ta tarihin da Atika ke fadi mata na game da rayuwarta kamar haka:

Atika jikar wani mutum ne da ake kira Hakilu mai baka, kuma maharbi ne, wanda shi kuma dan asalin wani kauye ne, Kwarin Gwauro, Arewa da birnin Kantuk. Ya tashi cikin talauci, cikin halin kaskanci. Don Atika na ba ta labarin, kakanta, kamar a ce shi ya yi wahalar kiwon akuyar da ya kai kasuwa ya sayar, kudin ya kai kasuwa kuma ya sawo talauci. Da abin ya ishe shi sai rannan ya yi ma wani malami alaramma magana da ya bashi taimakon wani fahami wanda za ya sha ya yi arziki. Malamin ya aminta, ya rubuta masa wani hatimi na Annabi Yusuf (AS) Lokacin da aka wanke aka kawo masa a cikin koko sai ya ajiye a cikin dakinsa, wai da zimmar idan ya dawo daga sallar azahar ya sha. Kafin ya dawo sai ita kuma Atika, sa’ilin ta na da shekara tara da haihuwa, kishin ruwa ya koro ta, ta shiga dakinsa ta ga wannan rubutu, ta yi zaton ruwan sha ne, sai ta dauka ta shanye. Da ya dawo ya nemi rubutu ya ga an shanye shi sai ya shiga cikin gida ya tambaya ko wanene ya shanye masa rubutun da Malam ya aiko masa? Sai ta ce ita ce. Sai ya ce ‘shikenan, ke Allah Ya yi wa arziki’. To tun daga sannan duk abinda ta sanya ma hannu sai ya yi albarka. Ko a cikin ‘yammata ta fi kowa tagomashi. Har aurenta ya zo ta na da abin hannunta don har bashi ta ke badawa.

To abinda ya jawo mata talauci daga baya shi ne sauyin zamani. Dama a kasar Hausa kwata, talauci na haddasuwa ta dalilai uku: na farko, zamani na sanyawa a wuce da yayin wata sana’a ta yadda mai yin ta saidai ya koma talaka. Misali: Atika ta yi sana’ar tufkar igiya, da ta ke ba yaranta samari, tun gabanin ma ta yi aure, su kuma su na zuwa kasuwa su na sayar mata. Ta samu arziki sosai da wannan sana’a. Amma a yau an wayi gari ina kasuwar riba ga wannan sana’a? Sai a dade ba a neme ta ba saboda yanzu an yi roba mai tsawo, inganci da kwari daga kamfunna.  Halisa ta ci gaba da ba Turai labari cewa Atika na shaida mata cewa a lokacin su, kafin ta yi aure ma sana’ar dako na kawo rufin asiri, kamar akwai maza da su ka yi fatauci tare, kusan dukansu sun yi sana’ar dako, kuma shi ya zama salar yin arzikinsu, amma yau, an wayi gari ina ma dakon ballantana ma ya yi tasiri? Saidai tsinta-tsinta. Tunda ga baburan okada ko’ina cikin karkara da maraya, ga Keke Napep nan ko’ina cikin birane. Sannan Atika ta shaida ma Halisa cewa abokan arzikinta a da, wasu sun yi sana’ar gini, wanda ake kwaba kasa ana yin tubulla. To yau zamani ya zo, ginin kasa na tubali saidai rauraye, don kusan duk an koma ga ginin siminti. To masu yin wannan sana’a idan ba sauyawa su ka yi zuwa ga ginin zamani ba saidai su yi bara.

Atika ta ci gaba da ba Halisa aminiyarta labari kamar yanda itama ta shaida ma Turai cewa shekaru ashirin da su ka gabata babu wuraren cajin wayar hannu ko salula a duk fadin kasar Langeri, babu kuma wuraren gyaran su, amma a yau an wayi gari samari sun mayar da wadannan sana’o’I, kuma akwai rufin asiri a ciki.

Jin haka sai Turai ta yunkura ta ruga kuryar daki ta dauko takarda da alkalami ta dawo da sauri ta zauna ta sanya dole saida Halisa ta yi mata tariya, ta rubuta don kada zancen ya bace mata. To wadannan sana’o’I da Atika ta yi a baya, a yau, duk zamani ya wuce da su, dole ta koma matalauciya. A bangaren ta kenan.

‘Shi kuma maigidanta Baballe direba’, Halisa ta ci gaba da ba Turai labari, ‘shima matalauci ne na har ba arziki ma, kamar ma mai bakin tauri. Amma shi talaucinsa ba irin na matarsa Atika ba ne, na shi na shu’umanci ko dabi’a ne. Watau a nan, ana nufin dabi’a ta halayya ta na tare da mutum, na babu sa’ar samun abin Duniya sam. Idan ma an samu, to babu albarka. Domin haka idan Baballe direba ya nema sai ya samu kadan ko ma ya rasa a sakamakon shu’umanci na jikinsa’. Wannan shi ne milasin sababun talauci a rayuwar Dan Adam na biyu. Abin da ke haddasa talauci na uku kuma shi ne na son jiki ko lalaci tunda dukkan samu na tare da nema, don ma Allah da kanSa Ya ce : ‘tashi in taimakeka’ To abin da Halisa ta lura, dukkan ‘ya’yan Atika gaba daya abinda ya haddasa masu nasu talaucin shi ne rashin nema da kuma lalaci. ‘Ya’yanta mazan duk barayi ne kuma ‘yan ta’dda. Jin haka, sai Turai ta buga kafa a kasa ta ce ‘kayya, an dai daba, wai mace ta haifi mace’.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: