Daga Muhammad Maitela, Damaturu
Kalaman ministar harkokin mata, Sanata A’isha Jummai Alhassan sun jawo muhawara mai zafi tare da jan hankulan manazarta lamurra da fashin bakin siyasa a Nijeriya. Zantukan sun tada kura musamman na kasancewar ta daya daga cikin yan majalisar zartaswan gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari. Duk da yadda a wani baren wasu na kallon furucin nata matsayin yaye labulen shafin alkiblar zaben 2019 mai zuwa.
A cikin hira da manema labarai, Sanata A’isha ta fito balo-balo inda ta bayyana goyon bayan ta ga tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abukakar a zabe mai zuwa na 2019. Alhassan ta bayyana dalilan ta na yin hakan, da nanata cewa shima shugaban kasa Muhammad Buhari ya san da cewa Turakin na Adamawa a matsayin maigidan ta ne. Yayin da ta saba misali da cewa mukamin da ma ya bata na ministar mata ba da ita yayi magana ba, da maigidan nata yayi, sannan ta ce wannan ra’ayin ta ne; duk da shi Atikun bai riga ya fito fili ya shelanta aniyar tsayawa takarar ba tukuna.
Maman Taraban ta ci gaba da fayyace wannan matsayar da ta dauka da cewar tayi hakan ne saboda sanin da tayi kan cewa Muhammad Buhari ya tabbatar musu ba zai tsayawa karo na biyu ba. Har wa yau, ta ce kuma koda ace zai tsaya to ita maigidan ta zata goyawa baya, kuma a shirye take ta ajiye masa aikin sa idan lokacin yayi da har suka tsaya tare. Sa’ilin nan ta tabbatar da cewa dama can gwamnatin Buhari ta gamin-gambiza ce; baya ga ministocin PDP da ake dasu, inda suma na APC din ma zaman yan-marina suke yi a junan su.
Tuni dai wadannan kalaman nata suka jawo tankiya da basu ma’anoni kala-kala. Amma dai masu fashin bakin al’amurran siyasa da yanayin da kan je ya dawo basu ga beken Santar ba, maimakon hakan jinjina mata suka yi tare da cewa ai kamar ankararwa ne. Basu tsaya nan ba, sun nuna yadda yan siyasa kan kai gwauro-mari idan irin wannan lokaci ya karato wasu kuma sun auna ikirarin tamkar yaye labulen alkiblar zabe mai zuwa ne.
Haka zalika kuma, duk da matsayar Ministar matan sun yi hannun-riga da ra’ayoyin.Inda a wani haujin kuma zantukan sun fito da wasu bayanan da ke ciwa jama’a da dama tuwo a kwarya. Wasu kuma suka samu damar dora ayoyin tambayar yadda tafiyar gwamnatin APC ke kwan-gaba kwam-baya da gano membibin majalisar zartswar Buhari gamin-gambiza ne masu kama da hatsin bara? Kuma, koba komai dai, duk abinda kaga ya kai bera wuta to ya dara wutar zafi.
Akwai masu hasashen cewa dama can sun san a rina. Tare da nuna cewa, ana zaton wuta a makera sai gata a masaka! Talakan Nijeriya ya zaku ya ga canjin da gwamnatin APC ta yi masa alkawari, amma har yanzu ba amo ba labari. Yayin da kuma har yanzu tsadar rayuwa sai kara ta’azzara take, kuma babu wasu alamu dake nuna cewa akwai yuwuwar samun sa’ida ga mai karamin karfi.
A cikin nashi ra’ayin, mai rajin tsarin dimokuradiyya Dakta Junaid Mohammed, ya bayyana wadannan kalamai na Hajiya Jummai Alhassan matsayin abin a yaba saboda yadda kalaman nata suka kunshi tsage gaskiya tsagwaron ta, kuma bata munafurci shugaban kasa ba.
“Abinda A’isha Alhassan ta bayyana ba wani bakon abu bane, a cikin ministocin Buhari nawa suka fadi irin wannan zancen a baya, kan cewa ba zai sake neman a zabe shi karo na biyu ba, bisa ga dalilan rashin lafiyar sa. “abinda minista Jummai Alhassan ta fada ba komai bane face gaskiya ce. Da yawa daga cikin ministocin Buhari sun fadi wannan zancen.Wannan gaskiya ce tsagwaron ta. Kuma ita kadai ce zata iya fitowa karara ta furta hakan, kuma bai kamata mutane su ga laifin ta”. Inji shi.
Har wala yau, Junaid Mohammed ya bayyana cewa sun tsammaci cewa Sanata A’isha zata yi murabus kafin ta furta wadancan kalamai, koba komai hakan zai kara armashi dangane da balagar siyasar Nijeriya a idanun duniya, amma babu wani laifi a demokudadiyance don mutum ya bayyana ra’ayin sa.
Tsohon mai baiwa Shehu Shagari shawarar ya nusar da cewa kamata yayi ace Alhaji Atiku Abubakar ya gamsar da yan Nijeriya musamman yan arewa dangane da dattakon sa, kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kafin a zabe shi a cikin kowanne mataki. Saboda shima ya sha fadar cewa yan Nijeriya sun zabi Buhari ba don kwararre ne ba face sai domin tsammanin dattaku a wajen sa.
“Wannan ba Wani abin damuwa bane dangane da sha’anin siyasa. Sai dai babban abin damuwa shi ne yan siyasar Nijeriya basu da akida ko yin wani abu domim talaka, suna yin wannan ne saboda neman mulki. Domin idan ba haka bane, kamata yayi Aisha Alhassan tayi murabus kafin tayi wadancan kalaman nata saboda kamar tana nuna gazawar gwamnatin Buhari ce tunda duk da tana karkashin gwamnatin sa amma tana hango Wani a wajen”. Inji Malam Lawan.
“Mafi yawan mutanen da Shugaba Muhammad Buhari ke aiki dasu na a cikin majalisar zartaswa ko a sauran ma’aikatu kusan duk na gamin-gambiza ne ne. Musamman da yake jam’iyyar APC hadaka ce, kaga ba dole sai ya san kowa ba”. Inji shi.
A hannu guda kuma, masanin kimiyyar siyasar yayi hasashen cewa akwai alamun a hakan za a tafi, sannan ya ce” akwai yuwuwar samun canje-canjen sheka daga wannan jam’iyyar zuwa waccac, musamman idan wasu yan siyasar suka hango cewa burin su ba zai cika ba na tsayawa takara. Saboda alamu suna nuna za a raba gari da wasu da dama a cikin jam’iyyar APC, kuma a PDP ma akwai yuwuwar hakan ya samu”.
“Sannan ka lura da wani abu guda daya, zai yi wahala ka ji zancen sake fasalin kasa idan ba zabe ne ya karato ba. Idan ka ji zancen Alhaji Atiku Abubakar da ya nuna goyon bayan sa ga yankin kudu maso-gabas wajen sake yiwa Nijeriya fasali, yayi wannan ne don ya samu goyon bayan al’ummar yankin. Gaskiya yan siyasar mu suna da gajen-hakuri wajen tantance manufofin su, sannan basu faye kallon abinda shi ne ra’ayin talakan Nijeriya ba, su dai barsu da ra’ayin kashin kan su”. Ya bayyana.
A ra’ayin kungiyar goyon bayan shugaban kasa Muhammad Buhari (Buhari Support Organisation) dake jihar Enugu, sun bukaci ministar sha’anin mata Sanata A’isha Aljassan da cewa tayi murabus bisa ga kalaman da tayi na cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin cewa sau daya zai yi mulki; ba zai tsayi karo na biyu ba. Sannan da zargin ta na fitowa karara ta goyi bayan Atiku Abubakar a zaben 2019 mai zuwa sabanin Buhari.
Shugaban ayarin, Chief Anike Nwoga ya bayyana hakan ga manema labarai a Enugun inda ya nuna cewa dama can ministan matan bata tare da gwamnatin Buhari.
“Daman mun riga mun sani kan cewa Alhaji Atiku Abubakar shi ne uban-gidan ta a siyasance amma ba zamu taba lamuncewa irin wadannan zantukan suka ga shugaban kasa Muhammad Buhari ba. Kuma wadannan zantuka nata sun bayyana karara kan cewa bata tare da gwamnatin Buhari saboda haka ban ga dalilin da zai sa ta ci gaba da kasancewa rike da wannan mukami na ta ba”. Inji shi.
“Saboda haka ta sauka kawai ta koma can domin ta ci gaba da yiwa gwanin nata yakin neman zabe. Amma a namu a gurin mu, Buhari yana da bukatar yin falan-biyu ne a karagar shugabancin Nijeriya domin aiwatar da manufofin sa, ba wai daya ba.