Connect with us

MAHANGA

Mamman Daura A Shekara 80

Published

on

Na san shi a tsawon rayuwana. Na tuna lokacin da nake makarantar Firamare, na ji mahaifina yana fada wa wasu abokansa cewa, an bai wa wani hazikin matashi mukamin Edita a jaridar New Nigerian, wanda zai maye gurbin Malam Adamu Ciroma. Malam Adamu, ya rike mukamin Edita na tsawon shekaru hudu, inda aka kara masa girma a matsayin babban Manaja. Malam Mamman Daura shi ne Editan da ya gaje shi.

A wannan lokaci, jaridar New Nigerian ta zama jirida ta farko a Nijeriya. A matsayina na yaro, na san abubuwa da dama a jaridar, ciki har da manyan ma’aikatansu. Mahaifina babban Edita ne, ina yawan ziyartar mahaifina a ofishinsa da niyyar ni ma ina sha’awar in zama kamar su idan na girma.

Ko da nake karamin yaro, ina karanta ra’ayin jarida wanda yake kadan a fejin jarida. Kowa yana karantawa. Candido ne ke yin wannan rubutu a ranar Laraba. Ban taba tunanin akwai mutum mai suna Candido sai da mahaifina ya fada min, inda ya bayyana min cewa, mutane da dama ne ke rubuta wannan ra’ayi a jaridar.

An nada Mamman Daura a matsayin Editan jaridar New Nigerian a shekarar 1969 lokacin da yake da shekaru 29 da haifuwa, tun wannan lokaci ne nake bin rubutunsa. Ya kasance yana ba ni sha’awa, a kodayaushe ina kokarin yin koyi da shi. Yana kara karfafa wa kamfanoni da gwamnati da kuma al’umma kwarin gwiwa wajen shugabanci.

Lokacin da yake babban Manaja, gwamnatin tarayya ta nada shi a matsayin mamba a kwamitin garan-bawul a tsarin mulki, wanda Cif Rotimi Williams ya zagoranta. Haka kuma an zabi Obafemi Awolowo da Aminu Kano a wannan kwamitin, amma daga baya Awolowo ya ki amsa.

Lokacin da na fara ganin sa ina dan shekara 20, tun daga lokacin ban sake ganin shi ba. Mun yi nisa da juna. Lokacin da muka hadu na farko, na fahimci duk abubuwan da ake fada min a kansa har ma da wasu karin abubuwa masu yawa. Shi mutum ne na musamman wanda ya samu horo. Zai iya sauraron maganar mutum na tsawon sa’a daya ba tare da manta abin da ya fadi ba. Haka kuma idan yana tattaunawa da mutum zai yi bayani cikin fahimta. Batun gaskiya, idan yana magana bai maimaita abin da ya riga ya fada. Akwai mutane masu hazaka, amma Malam Mamman mutum ne mai hazaka sannan kuma mutum ne mai fasaha, Mutum ne mai matukar tunani.

A zahirin gaskiya, shi mutum ne mai matukar hazaka,  tun yana Sakandare a garin Katsina, sannan ya koma Sakandare a garin Okene, yana daya daga cikin hazakakkun yaran Arewacin Nijiriya da Sardauna ya bayar da umurnin fitar da su waje domin su kammala karatunsu a can. Abokiyata, Marigayya Angela Durlong, tana yawan fada min cewa, mahaifinta, Ambasada Durlong Malamin Malam Mamman ne a makarantar Sakandare, yana fada mata irin baiwar da yake da ita a cikin yara.

Mamman mutun ne mai mayar da hankali kan abubuwan da suka shafe shi, bai damu da abin da ya shafi mutane ba, domin haka ne za ka same shi cikin barkonci. Wasu suna zargin sa a matsayin mutum mai girman kai, saboda ba ya shiga harkokin mutane da tare da dalili ba.

Amma ga wadanda suka sani, Malam Mamman mutum ne wanda ya kware wajen iya rubuta Turanci a kasar nan. A lokacin da Adamu Ciroma yake matsayin Editan New Nigerian yana yawan cewa, a wajen gudanar da aiki, Mamman Daura ya fi shi nesa ba kusa ba. Mutum mai bajinta ne kadai zai iya cewa wani ya fi shi. A lokacin da yake matsayin Edita, wasu masu basira daga yankin Kudu sun ce, Editan jaridar New Nigerian yana rubutu kamar Bature, saboda yadda ya kware wajen yin rubutu. Malam Mamman bai taba mayar da martini ba a ko’ina ko da kuwa yana da damar mayar da martanin.

Ina daya daga cikin ‘yan tsurarun ‘yan Nijeriya da suke ikirarin sun san Malam Mamman sosai. Mutane ‘yan tsiraru ne ke yin wannan ikirari. Shi mutum ne kamamme wanda ba ya zuwa wajen mutane barkatai. Abokansa ‘yan hadan ne kamar su Dakta Mahmud Tukur, wanda shi ma mutum ne haziki mai basira, wanda shi ne babban amininsa. Wadannan mutane suna matukar garmama maganarsu ko da kuwa sun yi ta ne cikin raha.

Mutane suna gina gidajen hutu ne domin su shakata, amma ban da irin su DaktaTukur, suna gina gidajen hutu ne domin su yi karatu. Na halarci taruka da dama a garin Kaduna, kodayaushe ina sha’awar kallon Dakta Tukur da kuma Malam Mamman suna tare.

Na tuna wani taro wanda ya gudana a shekarar 2002, ina tunanin Dakta Tukur ya makara bai iso wajen taron kan lokaci ba, sai na ji na firgita daga baya sai ga shi, inda a nan ne aka fara taron, Malam Mamman ya kalle shi ya ce, gaskiyar magana ya zo cikin kurarrar lokaci, kuma gaskiya ne an kusa tashi daga taro, sai mutane suka fara dariya.

Dakta Tukur mutum ne mai barkwanci shi ma. Kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya zama Shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2015, ya taba tambayar Dakta Tukur a kan su yi tafiya domin su je su ga abokinsa wani Tsohon soja a Anguwar Sarki da ke cikin garin Kaduna. Lokacin da suka isa, sai suka tarar da mutumin yana karatun Alkur’ani a dakinsa kusa da dakin awaki da akoyoyi da kuma kaji. Buhari da Dakta Tukur sai suka nemi waje suka zauna kafin mutumin ya kammala karatunsa. Lokacin da mutumin ya kamala, bayan sun gaisa, mituna kadan sai suka tafi. Suna kan hanyar dawowa, sai Buhari yana yabon mutumin a kan irin rayuwar da yake gudanarwa. “Wannan mutumin bai da matsala ko kadan” in ji Buhari. Dakta Tukur ya yi sauri ya ce, “ba haka ba ne, yana da matsaloli masu yawan gaske. Ta yaya wanda yake zaune kusa da awaki da kaji ka ce bai da wata matsala?” sai Buhari yana ta dariya har sai da suka iso gida.

A kodayaushe Mamman da abokinsa suna yin tunani ne a kan abubuwan da ke faruwa. Shi ya sa wadanda suka san su, to dole su san abokinsa, mutanen da suka san su kallonsu a matsayin mutune masu barkwanci. Malam Mamman ya ki amsar duk wani mukamin da gwamnati ta ke ba shi, tun da ya ajiye aiki a matsayin babban Daraktan jaridar New Nigerian, sai dai ya yi aiki na wani karamin lokaci. Na amince da shi a wannan bangaren. Ina yawan cewa, ya canza alkiblar wannan kasa kamar yadda yake.

Ina jin wani barkwanci a wajen sa, inda yake cewa, a yi amfani da rarar mai da Nijeriya ta ke samu wajen gudanar da duk manyan ayyuka. Mutane da yawa suna ganin hakan ba zai yiwa ba. Malam Mamman ya ajiye aiki a matsayin babban Daraktan jaridan New Nigerian bayan shekara uku da ba shi wannan mukami. Lokacin da Janar Murtala Muhammed ya hau kan karagar mulki, ya amshi kaso 60 na ayyukan jaridar Daily Times, sannnan ya amshi kaso dari bisa dari na jaridar New Nigarian.

Malam Mamman ya same shi, inda ya bayyana masa cewa, ba a wannan lokaci ya kamata ya aiwatar da wannan lamari ba. A lokacin ne ya ijiye aiki ya koma gudanar da kasuwancinsa. An ba shi mukamin Sarakta a kamfanin Nigeria Tedtiles Limited (UNTL). Lokacin da yake gudanar da harkokin kasuwancinsa, Kanal Muhammadu Buhari yana matsayin Kwamishinan man fetur a wancan lokacin. Malam Mamman bai da wata alaka da kamfanonin mai, maganar garkiya ma bai taba hada harkokin kasuwanci ba da wani kamfanin mai na kasar waje. Ko lokacin da Buhari ya zama shugaban PTF, kamfaninsa bai taba gudanar da wani aiki ba. Ya ce, bai kamata kamfaninsa ya gudanar da harkokin kasuwancin mai da wani kamfanin kasar waje ba ko kuma kamfaninsa ya gudanar da wata kwangila a karkashin PTF ba. Wannan shi ya sa abokantakarsu ta dore saboda mutumtawa da kuma girmama juna.

Ya samu gagarumar nasara a cikin harkokin kasuwancisa. Akwai ma lokacin shi ne yake jagorantar kasuwancin kamfanin Tadtiles a Arewacin Nijeriya gaba daya, kamar su Arewa Tedtiles, Funtua Tedtiles da kuma Fineted  a lokaci daya. Shi yake da kamfanin KFCC, kamfanin na daya wajen sarrafa katako a kasashen Afirka ta Yamma. Lokacin da kamfanin KFCC ya mutu ne aka samu manyan kamfanoni da bankuna a cikin wannan kasa. Haka kuma shi yake da kamfanin Kaduna Aluminum Ltd, da Kaduna Machines Works Ltd da dai sauran su. Shi ne kuma mai kamfanin BCCI wanda daga baya ya koma African International Bank da Hegemeyer da Dunlop da APICO Insurance da dai sauran su. Yana da hannun jari mai yawan gaske a kamfanoni masu gine-gine. Haka kuma ya taba rike mukamin shugaban NTA a wancan lokaci.

Lokacin da Malam Mamman ya fara ganina, ya dauke ni tamkai abokinsa, ina daukan kaina a matsayin babban yaro a cikin ‘ya’yansa, Mohammed da kuma kannansa, ba su da abin fadi sai abin da na ce. Halima wacce ita Likita ce tana ganin wasa ne. Halima ce ta fara fada min cewa, a yau baba zai cika shekara 80 a duniya. Taya Malam Mamman murnar zagayowar haihuwa ba abin da yake so mutane su sani ba ne. lokacin da ya fada min, sai na fara tunanin na samu abin da zan rubuta a kan shi. Wannan shi ne abin da na dade ina jiran ya kai shekara 80 da haifuwa.

Yana daukar duk abin da ya shafe ni da muhimmanci. Lokacin da mahaifina ya mutu shekara biyar da suka gabata, shi ne ya fara kirana. Yana daukar gidan jaridar LEADERSHIP a matsayin nasa, wanda yake alfari da shi. Yana matukar alfari da jaridar LEADERSHIP.

Kafin in fara wallafa jarida, ni ne Kakakin kungiyar ‘The Buhari Organization (TBO),’ muna gudanar da ayyukanmu cikin fushi, bayan da Tsohon Shugaban kasa, Obasanjo ya yi mana magudi a zabe, Malam Mamman da wasu suka ba ni shawarar in tafi kasar waje in samo Digiri na biyu a fannin aikin jarida, domin ban samu wani horo a aikin jarida ba, su suka kai ni waje. Yana jin tsoron kar a kashe ni, bayan an kashe Marshal Harry, Bola Ige, Aminosari Dikibo da dai sauran su. Yana kokarin kare lafiyata da rayuwata.

A shekarar 2003, lokacin da na fara kaddamar da LEADERSHIP CONFIDENTIAL, nan take ya biya kudin shekara biyu lokaci guda, bai yi tunanin ko gazawa ba wajen wallafa wannan jarida. Akwai lokacin da ya firgita da ni a shekarar 2003, ban taba manta wannan lokaci.

An samu masu biyan kudin jaridar LEADERSHIP CONFIDENTIAL kamar wutar daji. Mun samu masu biyan kudade daga waje, sai dai ba mu da asusu a kasashen waje. Na ziyarci kasar Ingila domin in bude asusun banki. Bankin da na ziyarta sun ki yi min abin da nake bukata, domin kasar Nijeriya tana karkashin su ne. shi ma Malam Mamman yana Ingila a wannan lokacin. Haka shi ma Sarki Abba yana kasar Ingila, inda ya fada wa wani abin da nake bukata.

Abin da ya faru shi ne, Malam Mamman da wannan mutumin sun rubuta wa Manajan bankin na Ingila a kan ya bude min asusu. Su ma Dakta Mahmud Tukur da Malam Musa Bello duk suna da asusun banki da su. Idan ba don su ba, babu yadda zan iya samun asubun bankin a kasar Ingila.

Lokacin da na isa bankin da wannan wasika, an dauke ni kamar wani mataimakin shugaban kasa, inda nan take aka bude min asusu. Daga nan ne na fara gudanar da babban kasuwancina. Kafin wannan lokaci, a wata rana a shekarar 2002, na ziyarci gidansa sai na ga an ijiye motoci da yawa. Na yi tunanin ana gudanar da wani taro ne, sai na tafi zuwa wani lokaci sai na sake dawowa. Ya bayyana min cewa, ai ya ganni lokacin da nake shigowa cikin gidan, inda ya umurci in dunga shiga ko da ana gudanar da taro ne. Ya dauke ni da matukar muhimmanci.

Akwai wani Sarki wanda ya taba ziyartar shi ba tare da sanin sa ba. Sai mai gadi ya fada masa cewa, akwai wani Sarki yana son ganin ka kuma yana bakin kofa. Ya yi matukar mamaki domin bai tunanin Sarkin zai ziyarce shi a wannan lokaci.

Abin mamaki Malam Mamman ya tafi kofa, bayan sun gaisa sai ya ce masa ba zai yiwu su shiga cikin gida ba, domin suna gudanar da wani taro kuma shi Sarkin bai sanar masa da zuwan sa ba. Sarkin ya juya shi da tawagarsa.

Idan kana son a san kowaye mutum, to ka duba su wa ne ne abokanansa.

Lokacin da ciwo ya yi wa Shugaba Yar’Adua tsaanani kuma komai zai iya faruwa, inda aka fara tunanin mulki zai bar Arewa, domin kauce wa zaben matamakin Shugaban kasa mara kwarewa, sai ni da Abba Kyari muka samu Janar TY Danjuma a kan mu gudanar da taron gaggawa tare da sauran manyan Arewa domin mu fitar da mataimakin Shugaban kasa. Nan take TY ya kara mana kwarin gwiwa. Malam Abba ya isa Kaduna, inda ya bayyana wa Buhari da Malam Mamman da Dakta Tukur da Malam Ahmed Joda da dai sauran su. Lokacin da ya isa Kaduna ya fara fada wa Malam Mamman a kan taron. Ba tare da wani tunani ba, sai Malam Mamman ya ce, ba a bukatar wannan taro a yanzu. Abin da zai faru shi ne, Janar Danjuma ya fitar da mataimakin Shugaban kasa a Arewa da kansa. Shi ma haka Dakta Tukur ya bayyana. Sai dai shi TY ya ce zai zabi kansa a matsayin mataimakin Shugaba Jonathan, wannan shi ne kawai matsala.

A wannan rana Buhari ya ziyarci Malam Mamman, sai Malam Abba ya jira shi domin ya isar masa da sakon. Lokacin da ya shiga ciki ba tare da sanin abin da Malam Mamman da Dakta Tukur suka fada ba, sai ya bayyana cewa, wanda ya amince ya zama mataimakin Shugaban kasa shi ne TY, Malam Abba ya yi dariya sai ya kirani. Ya bayyana min cewa, abin dariya ya faru, amma zai fada min komai idan ya iso garin Abuja. Haka shi ma Malam  Ahmed Joda ya fadi.

Malam Ahmed Joda mutum ne mai matukar daraja wanda ya sadaukar da rayuwansa wajen yi wa gwamnati aiki, sannan ya yi aikin jarida, yana kuma gudanar da harkokin kasuwancinsa, inda ya bayyana cewa, a zo gidansa domin gudanar da wannan taro. Lokacin da aka gudanar da sunan TY a matsayin wanda ake so ya zama mataimakin Shugaban kasa, ban ji wani ya kalubalanci hakan ba, domin dukkan su mabiya addinin Kirista ne. Ni ne mutumin da ya yi maganar a wajen wannan taro, inda na ce dukkansu Kiristoci ne koma ba zai harfar wa Nijeriya da mai ido ba.

Na bayyana cewa, kar mu damu da wanda ake so a baiwa, dukkan mu mun san waye TY. A wannan lokaci na san wasu mutane da ake kira da suna Kaduna Mafiya, na san suna da nasu ra’ayi. Ya kamata mu san abu mai kyau da kuma abin da ya dace ga Nijeriya. A wannan lokaci, an samu bayanan wannan labari a sirrance. TY da kansa ya nuna min labarin, sannan ya ce min ba shi da lafiya. Na yi dariya, sannan na ce masa mutanen da suka yi maka wannan bayanin ba su yi tunanin rashin lafiyarka ba. Mun ci gaba da tattaunawa har sai da Shugaba Jonathan ya kira TY da kansa, inda ya bukaci ya taimaka masa wajen zaban mataimakinsa a cikin Gwamnoni.

Bayan an zanta da wasu Gwamnonin, sai ya baiwa Jonathan sunaye guda uku wadanda suka hada da Babangida Aliyu; Gwamnan Neja, Namadi Sambo Gwamnan; Kaduna  da kuma Ibrahim Shema; Gwamnan Katsina. Babangida Aliyu bai cancanta ba, sakamakon bangaren da ya fito, saboda Shugaban Majalisar Dattawa, Dabid Mark dan Arewa ne kuma suna yanki daya na Arewa ta Tsakiya. Wannan dalilin ne ya sa aka zabi Namadi Sambo a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Bari in yi bayani a kan wasu ra’ayoyin da na samu. Da farko dai, Malam Mamman ba shi ke juya Shugaban kasa ba, wannan ba halinsa ba ne, Ko da wani ya yi kokarin juya Shugaban kasa, to sai ya yi kokarin tabbatar da cewa ba a juya Shugaban kasa ba. Maganar gaskiya, duk wanda yake tunanin cewa, za a iya juya Buhari, to bai san shi ba ne. Ana danganta shi a matsayin mutumin da bai iya canza ra’ayinsa. Idan da a ce Malam Mamman shi ke juya Shugaban kasa, ba za a taba tsare Sambo Dasuki ba. Saboda shi Sambo Dasuki surikin Malam Mamman ne kuma sun shaku sosai.

Wani abin kuma shi ne, Malam Mamman bai tilasta wa Shugaban kasa ya nada Abba Kyari a matsayin shugaban ma’aikarar fadar gwamnati a shekarar 2015 ba. Shugaban kasa ne ya fara kiran Malam Abba, sannan daga baya ya fada wa Malam Mamman a kan wannan mukami. Na san wannan ne saboda duk na san su. Lokacin da Shugaban kasa zai fara nada Ministoci, Malam Mamman bai da hannu wajen nada kowane Minista a cikin wannan gwamnati.

Gaskiya ne shugaban kasa da Malam Mamman suna da alaka, domin sun taso tare tun suna kanana. Su iyalai ne, amma kuma su abokai ne. Ya baiwa Shugaban kasa shekara uku, shi dai kawun Shugaban kasa ne a bangare daya. Saboda haka ne ma Shugaban kasa ya fi jin dadin kiransa da kawunsa, yana alfahari da shi a matsayinsa na kawunsa. Ni da Adamu Adamu muna yawan tsokanar su a kan haka. Suna da dangantaka mai karfi kuma ba sa rabuwa, ban taba ganin sun samu matsala ba. Kodayaushe Shugaban kasa yana yawan kare Malam Mamman.

Gwanda irin mutanen kirki kamar su Mamman Daura su kasance kusa da Shugaban kasa da irin su Dieziani ko kuma wasu bata-gari da suke kewaye da Obasanjo.

Jarumai kalilan ne suka rage a Nijeriya. Wannan ne muke bukatar kadan din da suka rake su kasance tare da mu a kodayaushe. Malam Mamman Daura yana daya daga cikin su.

Kamar yadda a yau ka cika shekara 80, addu’ata a gare ka, Allah ya kara maka tsawon kwana cikin koshin lafiya, domin ka ci gaba da yi wa kasa hidima.

Ranka ya dade ina taya ka murnar zagayowar ranar haifuwarka.
Advertisement

labarai