Wata cibiya mai nazarin kwallon kafa, CIES Obserbatory ta ce Manchester City kungiyar da take da ‘yan wasa masu tsada a tarihi a fagen tamaula.
City ta sayi ‘yan kwallo kan fam miliyan 215 a kasuwar da aka rufe a karshen watan nan, hakan ya sa ‘yan wasan kungiyar gabaki daya suka kai fam miliyan 775.
Manchester United ce ta uku a jerin kungiyoyin masu tsada, wadda jumullar farashin ‘yan wasanta fam miliyan 712. A bara ita ce ta daya, amma ta yo kasa saboda farashin ‘yan wasanta da kawai ya karu a bana.
Cibiyar ta CIES ta gudanar da bincikenta ne a Ingila da Faransaa da Jamus da Italiya da kuma Spaniya.