Rabiu Ali Indabawa">

MAN Ta Koka Da Yadda Ake Rarraba Wutar Lantarki A Nijeriya

Kungiyar masana’antu ta Nijeriya (MAN) ta koka ga yadda kamfanonin rarraba wutar lantarki(Discos) suka kasa dai-daita tsarin rarraba wutar lantarki a Nijeriya, inda wasu bangarorin suka fi wasu samun wutar lantarkin. A cewar shugaban kungiyar MAN, Injiniya Ahmed Mansur, ya ce, mun fahimma ana bai wa wasu yankuna wutar lantarki fiye da wasu bangarorin a cikin kasar nan, abin da ya fi ban takaicin ma dai shi ne, masu masana’antu suke biyan sabon karin kudin wutar lantarkin da yawa kafin su samu sarrafa kayayyakinsu zuwa kasuwa, sannan babu bambamci tsakanin masu samun wutar da wanda ba su samu wajen biyan kudi. Mansur ya bayyana cewa, biyan kudin wutar lantarkin ya sha bambam wanda wasu suke biyan sama da kashi 25, yana yi wa masana’antu wahala wajen gudanar da harkokinsu.

Ya ci gaba da cewa, ana samun bambanci a wajen biyan kudin wutar lantarki da kshi 25, wanda yake bai wa masana’antu wahala wajen iya gudanar da haekokin ksuwancinsu yadda ya kamata. Duk irin kokarin da masana’antu suka yi wajen kai korafinsu da kamfaanonin Discos, amma hakarsu bai cimma ruwa ba domin lamarin ya ci gaba da ta’azzara, hakan ya sa masana’antun suna tafka a sara wajen samun kudaden shiga. Ya ce, gwamnatin tarayya ta bai wa kamfanonin Discos damar rarraba wutar lantarki ne domin a samu dai-daituwa a ko’ina a fadin kasar nan, saboda dalilin samun damar dai-daita wutar lantarkin ga masana’antu a Nijeriya.
“MAN tana bukatar dai-daita biyan kudin lantarki duk da ana samu bambamce-bambamce wajen gudanar da harkokin sasuwanci. Ya kamata gwamnati ta shiga cikin wannan lamari tare da kawo karshen wannan matsala ta yadda za a samu dai-daituwar kudin wutar lantarki a cikin kasar nan.
“Domin haka, kungiyar MAN tana so ta yi amfani da wannan daman a goda wa gwamnatin tarayya wajen kokaarin farfado da tattalin arzikin kasar nan ta hanyar bunkasa fannin masana’antu a Nijeriya, musamman ma wajen inganta fannin wutar lantarki a cikin kasar nan.
“Rashin samun wutar lantarki yana daya daga cikin matsalolin da bangaren masana’antu suke fuskanta a wannan kasa, wannan ne ya sa masana’antu suke kashi kashi 40 wajen samar da wutar lantarki kafin sarrafa kayayyakinsu nay au da kullum a Nijeriya, wannan ne ya sa farashin kayayyaki suke hauhawa sama a kasar nan,” in ji shi.

Exit mobile version