Ammar Muhammad" />

Man United Ta Tabbatar Da Solskjaer A Matsayin Kocinta

Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United ta tabbatar da Ole Gunnar Solskjaer a matsayin kocinta na din-din-din inda ta kulla kwantiragin shekaru uku da shi.

Solskjaer mai shekaru 46 kuma dan asalin kasar Norway, ya karbi aikin kocin rikon kwarya a Old Trafford a cikin watan Disamba domin maye gurbin Jose Mourinho bayan kungiyar ta yi fama da rashin kokari.

Kocin ya sha kashi sau daya daga cikin wasanni 13 da ya jagoranci Manchester United a gasar firimiyar Ingila, kuma a halin yanzu tazarar maki biyu kacal ne tsakaninta da Arsenal da ke matsayi na hudu a teburin gasar.

Sannan kuma ya kafa tarihin zama koci na farko da ya lashe wasanni shida na farko a jere a Manchester United, inda ya sha gaban Sir Matt Busby.

Solskjaer ya shafe kakannin wasa guda 11 a matsayin dan wasa a Manchester United kuma shi ne ya jefa kwallon da ta bai wa kungiyar nasara a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai a shekarar 1999 tsakaninsu da kungiyar Bayern Munich.

Exit mobile version