Manchester City ta sayi dan wasan gaban kasar Masar, Omar Marmoush daga Eintracht Frankfurt kan Yuro miliyan 70.
Dan wasan mai shekaru 25 ya amince da kwantiragin har zuwa watan Yunin 2029, Marmoush ya zura kwallaye 15 a wasanni 17 da ya buga a gasar Bundesliga ta bana, kyaftin din Ingila Harry Kane ne kadai yafishi jefa kwallaye da ya ci wa Bayern Munich 16.
- Xi Jinping Ya Yi Rangadi A Arewa Maso Gabashin Kasar Sin Gabanin Bikin Bazara
- Dole Mu Bai Wa Matasan Nijeriya Dama A 2027 – Bafarawa
Marmoush ya ce “Manchester City tana daya daga cikin manyan kungiyoyi a duniya cikin shekaru 10 da suka gabata, don haka ba abin tambaya bane dalilin da ya sa na zo kungiyar, abin farin ciki ne kuma abin alfahari ne a gare ni da iyalina kasancewata a Manchester City”.
Marmoush ya fara sana’arsa ta kwallo da kungiyar Wadi Degla a gasar Firimiya ta kasar Masar kafin ya koma VfL Wolfsburg a 2020, ya yi zaman aro a FC St Pauli da VfB Stuttgart kafin ya koma Frankfurt a 2023, inda ya zura kwallaye 37 a raga kuma ya taimaka aka zura 20 a wasanni 67 da ya buga.
Ya zura kwallaye 20 a dukkan wasannin da ya bugawa Frankfurt a bana, kuma ana sa ran Marmoush zai buga wasan Firimiya da Chelsea a ranar Asabar, duk da cewa ba za a yi masa rajista ba a mako mai zuwa a gasar zakarun Turai da za su kara da Club Brugge, wanda dole ne City ta yi nasara don samun damar buga zagayen gaba.