Abba Ibrahim Wada" />

Manchester City Za Ta Iya Lashe Kofuna Hudu A Bana

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Bicent Kampany ya bayyana cewa kungiyarsa za ta iya lashe gaba daya gasanni hudu da take bugawa a wannan shekarar bayan sun samu nasara a wasan karshe na kofin Carabao akan Chelsea.
Manchester City sun samu nasarar lashe gasar cin kofin Carabao, bayan da a ranar Lahadi suka samu nasarar doke Chelsea a wasan karshe da suka fafata a katafaren filin wasa na Wembley dake birnin Landan.
A kwanakin baya dai aka bayyana cewa kungiyar ta Manchester City za ta iya lashe dukkanin kofunan da suke bugawa da suka hada da gasar firimiya da gasar zakarun turai da kuma kofin kalubale na FA.
“Yanayin yadda muke buga wasa da kuma nasarorin da muke samu zai tabbatar da cewa zamu iya bawa duniya mamaki ta hanyar lashe dukkan kofunan da muke bugawa na wannan kakar tunda yanzu mun fara da guda daya” in ji Kampany, dan kasar Belgium
Kafin a karkare wasan na karshe a ranar Lahadin sai da aka buga jimillar mintuna 120, wato mintuna 90 kamar yadda aka saba da kuma karin lokacin mintuna 30, ba tare da kowace kungiya tasamu nasarar cin kwallo ko da daya ba.
A zagayen bugun daga kai sai mai tsaron gida ne Manchester City ta doke Chelsea da kwallaye 4-3 sai dai rasa damar lashe gasar cin kofin Carabao ga Chelsea ya zo ne makwanni 2, bayan kaye mafi muni da kungiyar ta taba fuskanta cikin shekaru 28, a hannun Manchester City da ta lallasa ta da kwallaye 6-0 a fafatawarsu ta gasar firimiya.

Exit mobile version