Manchester United ta nemi da a ba ta faifan bidiyon da zai taimaka mata ta zakulo ‘yan kallon da suka ci zarafin Romelu Lukaku a karawar da kungiyar ta yi da Southampton a ranar Asabar.
Lukaku mai shekara 24, ya umarci ‘yan kallon kulob din na Manchester united da su daina cin zarafinsa a ranar Juma’a.
Sai dai kuma an rera wakar cin zarafin dan wasan a karawar da United ta ci Soutahmpton daya mai ban haushi a gasar Premier a filin wasa na St Mary a ranar asabar din data gabata.
A wata sanarwa da United ta fitar ta ce ‘’Kungiyar da dan wasan sun fayyace karara da a kawo karshen rera wakar cin zarafin da ake yi domin hakan bai kamata ba kuma zata hada kai da hukumar yaki da wariyar launin fata wato “Kick it Out” domin ganin an dauki mataki.
Magoya bayan United na yin kalamai kan girman mazakutar dan wasan gaban kungiyar ne wato Lukaku dan kasar Belgium.