Connect with us

WASANNI

Manchester United Bata Nemi ‘Yan Wasanmu Ba –In Ji Tottenham

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta bayyana cewa Manchester United bata nemi ‘yan wasanta ba duk da rade radin da aka dingayi na cewa United din ta nemi Toby Alderweid da kuma Danny Rose duka ‘yan wasan baya na kungiyar.
A kwanakin baya dai an danganta da dan wasan baya Toby Alderweid dan kasar Belgium da komawa Manchester United bayan da kociyan kungiyar ya bayyana cewa yanason siyan dan wasan baya a wannan kakar.
Shima dan wasan baya Danny Rose, dan kasar Ingila da yake buga wasa a kungiyar ta Tottenham an dangantashi da komawa Manchester United domin maye gurbin Luke Shaw wanda shima akayi hasashen zai bar United din.
“Manchester United bata nemi ‘yan wasanmu ba duk abinda ake maganar babu gaskiya aciki domin bamu hanasu ‘yan wasan muba kawai dai basuzo mana a hukumance bane sunce suna son siyan daya daga cikinsu” in ji wata majiya daga Tottenham din.
Shima dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Leceister City an danganta shi da komawa Manchester United sai dai shima tattaunawar bata kasance ba bayan da kungiyar ta Leceister City ta bayyana cewa dan wasanta bana siyarwa bane.
Mourinho dai yayi zargin cewa idan har kungiyar batayi kokari ba a wannan kakar laifin shugabannin kungiyar ne domin yace su siyo masa dan wasan baya amma basu siyo ba hakan yasa yaci gaba da amfani da wadanda yake dasu a kungiyar.
Advertisement

labarai