Kungiyar kwallon kafa ta Manchester united ta shirya tsaf domin taya dan wasan gaba na Juventus, Paolo Dybala a karshen kaka mai zuwa kamar yadda rahotanni suka bayyana daga kasar italiya.
Dan wasan dan shekara 21 dan asalin kasar Argentina ana dan gantashi da dan wasan Barcelona Leonel Messi wanda akace yana bawa dan wasan shawara daya koma Barcelona.
Rahotanni sunce Manchester united tanada niyyar biyan kudi fam miliyan 155 domin siyan dan wasan wanda ya zura kwallo 12 cikin wasanni 8 daya bugawa Juventus a wannan kakar.
Tuni akace shugaban gudanarwar Manchester united, Ed Woodward yafara tattaunawa da takwaransa na Juventus Beppe Marotta akan dan wasan.
Manchester united dai suna da kyakkyawar alaka da Juventus ta cinikayya batan da kungiyar ta siyi Pogba akan kudi fam miliyan 89 a kakar wasan data gabata.