Abba Ibrahim Wada" />

Manchester United Na Zawarcin Piatek Daga AC Milan

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta fara zawarcin dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta AC Milan, Krzysztof Piatek a watan Janairu mai kamawa idan an bude kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa.

A farkon wannan kakar ne dai kungiyar ta sayar da ‘yan wasan tan a gaba inda ta sayar da Rumelu Lukaku zuwa kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan yayinda shima dan wasa Aledis Sanchez ya bar kungiyar zuwa Inter Milan din a matsayin aro.

Tuni dai rahotanni suka bayyana cewa kungiyar Manchester United zata sayi dan wasan gaba a watan Janairu saboda dan wasan gaba, Marcus Rashford ya kasa daukar nauyin zura kwallo a raga kamar yadda kungiyar tayi tunani tun farko.

A kwanakin baya kociyan kungiyar ya bayyana cewa kungiyar zata nemi dan wasan gaba wanda zai taimaka mata kuma dan wasa Piatek shine wanda ake ganin kungiyar zata dauka domin ganin ta cigaba da zura kwallo a raga.

Dan wasan dai ya zura kwallaye 19 cikin wasanni 21 daya bugawa kungiyar Genoa a farkon kakar wasa ta 2018 zuwa 2019 kafin kuma ya koma AC Milan a watan Janairu na kakar inda ya zura kwallaye 13 cikin wasanni 28 daya buga a rabin kakar wasa.

Piatek, dan asalin kasar Poland ya buga wasanni 8 inda kuma ya zura kwallaye hudu kuma kawo yanzu yana da kwantiragin shekara uku a kungiyar ta AC Milan sai dai banda shi akwai dan wasan gaba na Lyon, Moussa Dembele da Mario Mandzukic na Jubentus da Manchester United duka tana zawarcinsu.

Exit mobile version