Manchester United Sun Yi Abin Kunya -KLOPP

Kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liɓerpool, Jurgen Klopp yace Manchester united sun bashi kunya bayanda ƙungiyar ta tsaya a baya taƙi fitowa a wasan da suka fafata a ranar asabar da rana.

Manchester united da Liɓerpool sun buga canjaras 0-0 a wasan sati na 8 da suka buga a filin wasa na Anfield wasanda Klopp din yace united sun yi abin kunya.

Liɓerpool ce dai ta mamaye wasan kusan tun lokacin da aka fara bugawa kuma ta samu hare-hare da dama sai dai basuyi amfani dasu ba sakamakon ƙoƙarin da mai tsaron ragar united din, daɓid de gea ya yi na hana ƙwallo shiga ragarsa.

Sai dai kociyan Liɓerpool, Jurgen Klopp, yace wannan abin kunya ne domin bai kamata ace ƙungiya kamar united tana buga salon irin wannan wasan ba.

Yace, yakamata su fito kamar yadda muka fito kowa ya nemi maki uku domin shi neabin da kowa yakeso kuma kowa zai iya samu idan ya yi amfani da damar da ya samu.

Ya ci gaba da cewa amma abin da sukayi abin kunya ne domin ƙungiya kamar Manchester united wadda take neman manyan kofuna yakamata a ce tana fitowa domin neman ƙwallo.

Yace, duk da cewa sune a gida saboda haka suna da dama wadda tafi ta united, amma duk da haka bazai iya yiwa yan wasan united alƙalanci ba saboda ba shi nemai koyar da ƙunhgiyar ba.

A ƙarshe klopp yace idan shi neya buga irin wannan salon ya san zaisha surutu amma saboda mourinho ne babu matsala saboda ba sabon abu bane a wajensa.

Mourinho dai ya lashe wasa ɗaya cikin wasanni  takwas da suka hadu da klopp inda aka yi canjaras guda huɗu a ciki.

Exit mobile version