Manchester United Ta Dauki Jadon Sancho

Daga Abba Ibrahim Wada

kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta amince da kudin da Borussia Dortmund ta gindaya, domin daukar dan wasan tawagar Ingila, Jadon Sancho, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Manchester United dai za ta biya kungiyar Borussia Dortmund kudi har fam miliyan 73 kudin dan wasan mai shekara 21 a duniya, wanda ya koma Jamus da buga wasa daga Manchester City a shekarar 2017.

Wannan labari ne mai faranta ran kociyan kungiyar ta Manchester United Ole Gunnar Solskjaer, wanda ke son bunkasa tawagar, domin taka rawar gani a kakar da zamu shiga a watan Agusta mai zuwa.

Manchester United ta yi ta biyu a gasar Premier League, wadda Manchester City ta lashe kofi na uku cikin shekara hudu, kuma United ta kai wasan karshe a Europa League da Villarreal ta lashe.

Tun farko kocin United ya fayyace gurbi hudu a kungiyar da yake son toshe baraka da suka hada da gefen hagu daga gaba da mai tsaron baya daga tsakiya da mai wasa daga tsakiya da mai cin kwallaye.

Tun a bara Manchester United ta yi niyyar sayen dan wasan, amma Borussia Dortmund taki amincewa ya bar buga gasar Bundesliga sakamakon kin rage farashinsa amma a wannan shekarar sun daidaita.

Da wannan cinikin zai zama dan Ingila mafi tsada a duniya, bayan Harry Maguire, wanda ya koma Manchester United daga kungiyar kwallon kafa ta Leicester City kan fam miliyan 80 a Agustan shekara ta shekarar 2019.

Sancho ya ci kwallo 50 ya kuma bayar da 57 aka zura a raga a wasanni 137 da ya yi wa Dortmund, wanda ya ci biyu a German Cup wasan karshe, inda mai buga gasar Bundesliga ta doke RB Leipzig a 4-1 a cikin watan Mayu.

dan kwallon ya buga wa tawagar Ingila wasanni sau 20 tun da ya fara buga mata wasa a shekarar 2018, ya kuma ci kwallo uku, yana cikin masu buga mata gasar Turai ta Euro 2020 da a yanzu haka ake fafatawa.

Tuni wasu rahotanni suka bayyana cewa dan wasan zai saka riga kai lamba 7 a kungiyar wadda a yanzu haka dan wasa Edinson Cabani ne yake sakawa sai dai har yanzu babu tabbas ko Cabani zai hakura ya bayar da rigar ga matashin dan wasan.

Exit mobile version