Connect with us

WASANNI

Manchester United Ta Fara Zawarcin Ozil A Karo Na Biyu

Published

on

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta fara zawarcin dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mesut Ozil bayan da aka bayyana cewa har yanzu akwai rashin jituwa tsakanin dan wasan da kociyan kungiyar.

A watan Janairun daya gabata ne dai Mourinho yaso ya siyi dan wasan daga Arsenal sai dai daga baya dan wasan ya sake sabon kwantaragi da kungiyar inda kungiyar za ta dinga bashi albashin fan dubu dari uku da hamsin a duk mako (350,000)

Mourinho dai ya taba aiki da Ozil a lokacin da suka yi zaman kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid kuma yaso daukar dan wasan tare da abokin wasansa Aledis Sanches sai dai daga baya Ozil din ya sake sabuwar yarjejeniya da Arsenal din a lokacin tsohon kociyan kungiyar Arsene Wenger.

Tun a farkon fara kakar wannan shekarar ne dai wasu rahotanni suka bayyana cewa akwai rashin jituwa tsakanin dan wasa Ozil da kociyan kungiyar Unai Emery sai dai daga baya Ozil din ya kartaya zancen inda yace babu wata matsala da take tsakaninsa da sabon kociyan.

Shima kociyan kungiyar ya bayyana cewa shi da Ozil suna zaman lafiya kuma suna girmama juna babu wani rashin jituwa duk da cewa a kwanakin baya ya fito ya soki Ozil akan cewa dole sai ya dage yayi wasa da karfinsa idan har yanason yaci gaba da buga wasa a kungiyar.

Ozil mai shekara 29 a duniya wanda a kwanakin baya yayi ritaya daga bugawa kasarsa ta haihuwa wato Jamus wasa ya zura kwallo a wasansu na wannan makon da kungiyar Newcastle a wasan da suka tashi daci 2-1
Advertisement

labarai