Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta saka dan wasan ta na gaba, Rumelu Lukaku a kasuwa a kakar wasa mai zuwa domin karawa acikin kudin da zata ware domin siyan sababbin ‘yan wasa kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Manchester United ta biya fam miliyan 75 ga kungiyar kwallon kafa ta Eberton domin siyan dan wasan na gaba a lokacin tsohon kociyan kungiyar Jose Mourinho wanda kungiyar ta kora a watan Disambar shekarar data gabata
Kungiyar dai ta shirya rabuwa da wasu daga cikin manyan ‘yan wasanta masu daukar albashi mai yawa kuma Lukaku yana daya daga cikinsu bayan da tun bayan da Mourinho ya bar kungiyar baya samun wasanni akai-akai.
Acikin watanni biyu da Solkjaer yayi yana jagorantar kungiyar Lukaku sau uku yafara buga wasa acikin ‘yan wasa 11 na farko kuma guda biyu a gasar cin kofin kalubale na FA ne da kungiyar ta buga sai guda daya a kofin firimiya.
Manchester United tana fatan ganin ta siyi dan wasan gaba wanda zai dinga zura kwallo a raga inda tuni ta fara tunanin neman dan wasan gaba na Inter Milan, Mauro Icardi, dan kasar Argentina wanda kungiyoyi da dama suke nemansa.
Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa tsohon dan wasan na Chelsea da Eberton wato Lukaku, yafi son komawa kungiyar kwallon kafa ta Jubentus dake kasar Italiya yayinda daman Manchester United tana neman dan wasan kungiyar Paulo Dybala.