Manchester United Ta Sake Kai Tayin Kudin Sancho

Sancho

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sake kai tayin kudi Fam miliyan 75 domin sayen dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund Jardon Sancho, wanda kuniyar ta nema ruwa a jallo a kakar wasan data gabata.

Tun a kakar wasan da ta gabata ne dai Manchester United take zawarcin dan wasan na Ingila wanda har yanzu bai bugawa tawagar ‘yan wasan kasar Ingila wasa ba a wasannin da ake fafatawa na kofin nahiyar Turai.

A kakar wasan da ta Manchester United ta yi zawarcin matashin dan wasan mai shekara 21 a duniya sai dai Dortmund ta yi masa farashin fam miliyan 108, farashin da Manchester United ta ce ya yi mata tsada duba da halin rashin kudin da kungiyoyin duniya suka shiga sakamakon annobar cutar Korona data talauta da yawa daga cikin kungiyoyin.

Sai dai a wannan lokacin Manchester United ta koma inda ta yi tayin farko Dortmund din ta yi fatali da shi, amma kamar yadda rahotanni daga kasar Jamus suke bayyana wa kungiyar ta Ingila ta yi tayin da abu ne mai wahala Dortmund din ta yi fatali da shi na Fam miliyan 75.

Tuni dai aka kulla yarjejeniyar albashi tsakanin Sancho da Manchester United tun a shekarar da ta gabata, kuma ana ganin gaba daya kungiyoyin guda biyu suna ganin a wannan lokacin cinikin zai iya fadawa na dan wasan wanda a baya lokacin da yana matashin dan wasa ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester City.

Ban da Manchester United, kungiyoyin Real Madrid da Chelsea da Liverpool da tsohuwar kungiyarsa ta Manchester City duka suna zawarcin Sancho, sai dai a zuciyarsa ya fi son bugawa Manchester United kuma ita ma kungiyar ta fi bukatarsa sama da ragowar kungiyoyin

Exit mobile version