Manchester United Ta Shirya Sayen Sancho Kan Yuro Miliyan 100

Kungiyar Manchester United har yanzu tana nuna sha’awarta kan siyan dan wasan kungiyar Dortmund, Jadon Sancho kan kudi Yuro miliyan 100 kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Dan wasan Sancho, yana nuna kwarewa a matsayin matashin dan wasa mai kwazo, inda ya zura kwallo 18 tare da taimakawa a ci kwalllo har 30 a fita 68 a gasar Jamus.

‘Dan wasan mai shekara 19, kungiyar Borussia Dortmund  tana neman kudi a hannu ne, wanda dan wasan ya bar Manchester City akan Yuro miliyan 8.

Borussia Dortmund ta ce a shirye suke su siyar da dan wasan ga kungiyar kasar Ingila.

Exit mobile version