Abba Ibrahim Wada" />

Manchester United Tana Magana Da Griezman

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta tuntubi dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Antonio Griezman domin ya koma kungiyar bayan day a bayyana cewa zai bar kungiyarsa a karshen wanann kakar.
A kwanakin baya ne dai dan wasan dan asalin kasar Faransa ya bayyana cewa zai bar kungiyar Atletico Madrid bayan ya shafe sama da shekara biyar a kungiyar inda ya zura kwallaye 133 cikin wasanni 257 daya bugawa kungiyar.
A kwanakin baya aka bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ce akan gaba wajen neman dan wasan inda kuma aka tabbatar da cewa sun fara Magana da dan wasan akan komawar tasa filin wasa na Nou Camp.
Sai da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, wadda ta kusa siyansa a kwanakin baya ta koma nemansa inda aka bayyana cewa zasu iya biyan fam miliyan dari da hudu da ake bukata ga duk kungiyar da take son siyansa.
Har ila yau wasu rahotanni sun bayyana cewa kungiyoyin Real Madrid da Manchester City basa daya daga cikin kungiyoyin da suke neman dan wasan yayinda itama PSG tace bata bukatarsa a yanzu hakan yasa Manchester United akan gaba a cikin kungiyoyin da suke zawarcinsa.
Har ila yau wasu rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta taya dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Lyon, Moussa Dembele inda aka bayyana cewa sun taya shi fam miliyan 40.

Exit mobile version