Connect with us

WASANNI

Manchester United Za Ta Hakura Da Neman Grealish

Published

on

kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta hakura da neman dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa, Jack Grealish, bayan da kungiyar ta tsallake siradin faduwa daga gasar firimiyar Ingila a ranar Lahadin data gabata.
Tun farkon wannan kakar aka fara danganta Grealish da komawa Manchester United sai dai sakamakon kungiyar ta Aston billa yanzu zata ci gaba da buga gasar firimiya ta Ingila bayan tasha da kyar a wasan karshe zata tsugawa dan wasan kudi.
Bayan an tashi daga wasan da Aston billa ta buga 1-1 da West Ham United ne a wasan karshen da suka fafata a ranar Lahadin da ta gabata dan wasan wanda ya zura kwallon da kungiyar taci ya bayyana cewa bai san kungiyar da zai buga wa wasa ba a kakar wasa mai zuwa.
Sakamakon nasarar da Aston billa ta samu na ci gaba da zama a gasar firimiya har zuwa kakar wasa ta gaba ana ganin kungiyar zata so ci gaba da zaman dan wasa Grealish idan kuma Manchester United ta takura akan dan wasan dole sai ta biya fam miliyan 80 a cewar wasu rahotanni.
Tuni aka bayyana cewa Manchester United ta fara jan kafa akan cinikin dan wasan inda wasu rahotanni suka bayyana cewa shugabannin kungiyar sun karkata akalarsu a yanzu wajen ganin sun sayi dan wasan Borussia Dortmund, Jardon Sancho, wanda shima kungiyar ta dade tana zawarci.
Har yanzu dan wasan yana da ragowar kwantiragin shekara uku a kungiyar sai dai baya tunanin sake sabuwar yarjejeniya kuma yana son buga wasa a kungiyar da take buga kofin zakarun turai a kakar wasa mai zuwa kamar yadda wakilin dan wasan ya bayyana a kwanakin baya.
Grealish wanda shine kaftin din kungiyar ya buga wasanni 36 a kungiyar ta Aston billa a kakar wasan shekarar nan ta 2019 zuwa 2020 inda ya zura kwallaye takwas sannan ya taimaka aka zura kwallaye shida a raga kuma yana fatan kociyan tawagar Ingila zai gayyace shi a wasan da kasar zata fafata a nan gaba kadan.
Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United dai ya bayyana cewa zai sayi ‘yan wasa domin kara karfi a kakar wasa mai zuwa inda a halin yanzu kungiyar take son sayan dan wasa Jardon Sancho wanda shima dan kasar Ingila ne daga Borussia Dortmund.
Manchester United ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin zakarun turai bayan masarar data samu akan kungiyar Leceister City a ranar Lahadi sannan kuma kungiyar zata ci gaba da buga gasar cin kofin Europa wanda za’a ci gaba a watan Agustan nan.
Advertisement

labarai