Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Robert Pires, ya bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United zata iya bawa duniya mamaki ta hanyar lashe gasar firimiyar Ingila ta bana da ake bugawa.
Manchester United ta sake karbe jagorancin gasar Premier Ingila bayan da ta doke kngiyar Fulham har gida da ci 2-1, yayin fafatawar da suka yi a daren ranar Laraba wasan da United din tasha da kyar.
Kungiyar Fulham ce ta soma jefa kwallo a raga, kafin daga bisani Manchester United ta rama ta kuma kara guda daya ta hannun ‘yan wasanta guda biyu da suka hada da Edinson Cabani da kuma Paul Pogba.
A yanzu Manchester United ke jagorancin gasar Premier da maki 40, Manchester City da itama a ranar Laraba ta doke Aston Billa da ci 2-0 na biye da maki 38 a matsayi na biyu sai kuma Leicester City itama da maki 38 a matsayi na 3, yayin da Liberpool ke da maki 34.