Abba Ibrahim Wada" />

Manchester United Za Ta Nemi Mandzukic

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tana shirin tuntubar kungiyar kwallon kafa ta Jubentus akan dan wasan gaba na kungiyar Mario Mandzukic dan kasar Crotia.
Manchester United dai batada karfi a bangaren ‘yan wasan gaba sosai bayan da kungiyar ta siyi dan wasa Aledis sanches daga kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a watan Janairun daya gabata sai dai watakila kungiyar za ta kara dan wasan gaba musamman idan dan wasa Martial yabar kungiyar.
Rahoton ya ce Mourinho yana son dan wasa Mandzukic kuma nan gaba kadan zai tuntubi kungiyar Jubentus akan ko zasu siyar masa da dan wasan wanda yashafe shekaru uku a kungiyar kuma ya zura kwallaye da dama.
Mandzukic, mai shekaru 32 a duniya ya buga wasanni 127 sannan ya zura kwallaye 33 a kungiyar kuma a yanzu haka yana kasar Rasha inda yake wakiltar kasarsa ta Crotia a gasar cin kofin duniya da a yanzu haka yake gudana.
Har yanzu dan wasan yanada ragowar kwantaragin shekaru biyu a kungiyar Jubentus sai dai kungiyar za ta iya siyar dashi idan har ya nuna cewa yanason barin kungiyar zuwa Manchester United bayan kammala gasar cin kofin duniya.

Exit mobile version