Abba Ibrahim Wada" />

Manchester United Za Ta Nemi Timo Werner

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United zata nemi dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig, Timo Werner, domin ya koma kungiyar a watan Janairu mai zuwa duk da cewa Liverpool itama tana zawarcin dan wasan gaban.

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen ta kusa daukar matashin dan wasan mai shekara 23 a duniya kafin a fara kakar wasa ta bana sai dai daga baya cinikin bai kasance ba kuma ya sake sabuwar yarjejeniya da kungiyarsa.

Sai dai tun a kwanakin baya aka fara danganta dan wasan da komawa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, wadda itace a mataki na farko a gasar firimiyar Ingila sai dai yanzu Manchester United, wadda take neman dan wasan gaba ruwa a jallo ta shiga neman dan wasan.

Kamar yadda rahotanni daga kasar Ingila suka ruwaito, kungiyar kwallon kafa ta Manchester United zata nemi dan wasan a watan Janairu mai zuwa kuma farashin dan wasan zai kai fam miliyan 27 ga duk kungiyar da zata iya biya.

Ana ganin dai idan har Manchester United ta nemi matashin dan wasan zai amince da zuwa saboda idan ya shiga kungiyar a yanzu zai samu damar buga wasa duk sati saboda babu cikakken dan wasan gaba kawo yanzu a United din.

Kawo yanzu dai Werner ya zura kwallaye 13 cikin wasanni 15 din daya bugawa kungiyarsa ciki har da kwallaye ukun daya zura  a ranar Asabar a wasan da kungiyarsa ta samu nasara akan kungiyar Meinz daci 8-0.

Exit mobile version